Fadar Shugaban kasa: Miyetti Allah ma kungiya ce kamar ta Ohanaeze Ndigbo da Afenifere

Fadar Shugaban kasa: Miyetti Allah ma kungiya ce kamar ta Ohanaeze Ndigbo da Afenifere

- Kakakin Shugaban kasa, Garba Shehu yace kungiyar makiyaya ta Miyetti Allaj ma kungiyar al’ada ce a kasar

- Garba ya kuma karyata cewa gwamnatin tarayya ta biya kungiyar makudan kudi don tausar su

Hadimin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya alakanta kungiyar makiyaya ta Miyetti da kungiyoyin Ohanaeze Ndigbo da Afenifere.

Yayin da ya bayyana a shirin Channels TV na Sunrise Daily a ranar Talata, yace kungiyoyin basu da alaka da ayyukan ta’addanci.

Hadimin shugaban kasar ya amince cewa gwamnatin tarayya na adaka da shugabancin kungiyoyin.

Fadar Shugaban kasa: Miyetti Allah ma kungiya ce kamar ta Ohanaeze Ndigbo da Afenifere

Fadar Shugaban kasa: Miyetti Allah ma kungiya ce kamar ta Ohanaeze Ndigbo da Afenifere
Source: Twitter

Tattaunawan ya biyo bayan rahotannin hare-hare da makiyaya suka daukaka wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma asaran kaddarori.

A lokacin da aka tambaye shi ko Gwamnatin Tarayya ta baiwa kungiyar MACBAN kudi don kwantar hankali, ya musanta hakan, inda yake fadin cewa: "wannan tamkar karya ce. A dukkan tattaunawa da muka yi da su, ba ayi zancen kudi ba.”

KU KARANTA KUMA: Sabon majalisar Buhari: Yan siyasa 15 na kamun kafa domin samun kujerar minista a wata jihar Kudu

Garba Shehu, Babban Hadimin Shugaban Kasar yace anyi tattaunawan ne don baiwa shugabancin kungiyar damar yin gargadi ga mambobin ta.

Ya bayyana cewa kasancewa akwai wasu bata gari cikin kungiyan bai bada damar jingina laifi ba akan sauran mambobin kungiyar ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel