Buhari ya gana da shugabannin tsaro cikin fadar Villa

Buhari ya gana da shugabannin tsaro cikin fadar Villa

A yayin ci gaba da daurin damarar kawo karshen kalubalai na rashin tsaro da ya zamto alakakai a kasar nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talatar da gabata cikin fadarsa ta Villa ya gana da shugabannin tsaro na kasa.

Buhari ya gana da shugabannin tsaro cikin fadar Villa
Buhari ya gana da shugabannin tsaro cikin fadar Villa
Source: Facebook

Ganawa ta gudana tsakanin shugaban kasa Buhari da dukkanin shugabannin hukumomin tsaro na kasa domin tumke damara da tattauna batutuwa dangane da yadda za a kawo karshen annobar ta’addanci a fadin kasar nan.

Majalisar hukomomin tsaro da ta gana da shugaban kasa Buhari cikin fadar sa ta hadar da; shugaban ma’aikatan dakarun tsaro Janar Gabriel Olanisakin, shugaban sojin kasa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, shugaban sojin sama Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas da kuma shugaban sojin sama, Air Marshal Abubakar Sadique.

KARANTA KUMA: Mu na iyaka bakin kokari wajen inganta tsaro a Najeriya - Babban Sufeton 'Yan sanda

Sauran wadanda su ka halarci taron sun hadar da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, mai ba kasa shawara a harkar tsaro Babagana Monguno, Ministan tsaro Mansur Dan Ali, shugaban hukumar leken asiri NIA, Ahmed Abubakar, sufeto janar na ‘yan sanda Muhammadu Adamu da kuma shugaban hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS , Yusuf Magaji Bichi.

A yayin da makamancin wannan taro ke gudana akai-akai, ku tuna cewa a baya jaridar Legit.ng ta kawo rahoton cewa shugaban kasa Buhari a ranar Talata, 5 ga watan Maris da ta gabata ya yi ganawar sirri da shugabanni tsaro na kasar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel