Kotun Shari'a za ta datse hannun mutum 10, a jefe 5 a Bauchi

Kotun Shari'a za ta datse hannun mutum 10, a jefe 5 a Bauchi

Shugaban gidan yarin Bauchi, Suleiman T. Suleiman ya ce mutane biyar da aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar jifa da wasu 10 da za a datse wa hannaye da kafufuwa suna nan suna jiran ranar da za a zartar da hukuncin.

A hirar da Suleiman ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke gidan yarin Bauchi a ranar Talata, ya koka kan yadda wadannan fursunonin da aka yanke wa hukunci suke zaune a kurkuku na tsawon shekaru 10 ba tare da an zartar musu da haddin ba.

Ya ce akwai wasu fursunonin shida da aka yanke wa hukuncin kisa, akwai wasu biyar da ake yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai sannan akwai wasu 188 da ake yanke wa hukuncin shekaru biyu da fiye da hakan.

Kotun Shari'a za ta datse hannun mutum 10, a jefe 5 a Bauchi

Kotun Shari'a za ta datse hannun mutum 10, a jefe 5 a Bauchi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya

Suleiman ya yi korafi kan cinkoso da ake fama da ita a gidan yarin inda ya ce an tsara gidan yarin ne domin mutum 500 amma yanzu akwai fursunoni 947.

Ya ce: "Mafi yawancin su kotun shari'a ce ta yanke musu hukuncin kisa. Akwai wasu kuma da ake yanke wa hukuncin datse hannaye ko kafafuwa amma suna zaune a gidan yari fiye da shekaru 10 ba tare da sannin matsayin su ba.

"Ba datse hannun su ba, ba a datse kafafuwan su ba, ba su san matsayar su ba.

"Akwai wadanda aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar jifa. Lamarin yana damu na.

"Zuciya ta tana sosuwa duk lokacin da na kai ziyara gidajen yarin domin sukan taso su tambaye ni halin da suke ciki.

"Na rubuta wasika ga gwamna da Alkalin Alkalai na jiha domin neman a dauki mataki a kan su.

"Ba za a iya kai su kotu ba saboda an yanke musu da hukunci sai dai ba a zartas da hukuncin ba."

Shugaban na gidan yarin ya ce idan ba za a iya zartas musu da hukuncin ba ana iya sauya hukuncin su zuwa zaman gidan yari.

"Idan hakan ba zai yiwu ba, sai ayi musu afuwa a kuma basu horro na sauya halaye sannan a sake su.

"Ina bukatar gwamnati ta zartas da hukuncin idan kuma hakan ba zai yiwu ba doka ta bawa gwamna ikon yi musu afuwa."

A cewar Majalisar Dinkin Duniya zartar da hukuncin kisa cin zarafi ne na bil adama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel