Matsalar rushewar gidaje: Jihohin Legas, Anambra da Abuja na kan gaba

Matsalar rushewar gidaje: Jihohin Legas, Anambra da Abuja na kan gaba

- Jihohin Legas, Anambra da Abuja na kan gaba

- Rashin sa ido wurin aikin ruguje gidaje, yin amfani da kayan aikin da ba su da inganci da kuma rashin hada kankare da kyau.

An fitar da sabuwar kididdigar dake nuna cewa jihohin Legas, Anambra, Kogi da babban birnin tarayya Abuja na kan gaba wurin samun matsalar rushewar gidaje, daga shekarar 2012 zuwa 2019.

Wani binciken da jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa kusan mutane 408 suka rasa rayukkansu, kuma sama da mutane 617 suka samu raunuka. Sauran jihohin dake da matsalar sun hada da Ogun, Kaduna, Taraba, Kwara, Benin, Abia, Ondo, Plateau, Rivers, Bayelsa da Sakkwato. Wasu jihohin dake da matsalar kuma sune, Benue, Oyo, Kano, AkwaIbom, Jigawa, Rivers, Neja da Osun.

Yayinda jihar Legas ke da matsalar rushewar har 38 a cikin shekarun da aka fitar da kididdigar, Anambra nada 10, Abuja 7, Kogi 7. Sai kuma jihohin Ogun, Kwara, Imo da Benue da kowace ta samu matsalar sau ukku cikin shekaru takwas, Su kuma jihohin Benin, Ondo, Delta, Akwa Ibom da kowace ta samu matsalar sau biyu a cikin shekarun. Su kuma jihohin, Kaduna, Taraba, Abia, Plateau, Rivers Bayelsa, Sokoto, Oyo, Kano, Jigawa, Neja kowace ta samu matsalar faduwar gini sau daya a cikin shekaru takwas.

KU KARANTA: Buhari yayi juyayin rashin wata ‘yar siyasar dake matukar mara masa baya

Wani rahoton da jaridar LEADERSHIP ta samu daga Cibiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NICE) ya bayyana cewa a shekarar 2012, mafi yawan rasa rayukkan da aka samu shine lokacin da wani gidan sama mai hawa ukku a layin Oloto dake Ebute Metta ya rushe kuma mutane goma suka rasa rayukkansu. Kusan mutane 24 suka mutu wasu 133 suka samu raunuka a cikin jihohin 25 a cikin shekarar 2012.

An alakanta wadannan matsalolin da rashin sa ido wurin aikin ruguje gidaje, yin amfani da kayan aikin da ba su da inganci da kuma rashin hada kankare da kyau.

Wasu masana da suka zanta da jaridar LEADERSHIP sun nemi a rika yin nazarin ingancin muhalli a kowane wurin da za a yi gini kafin a fara aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa

Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel