Buhari da APC ne ya kamata su dauki alhakin rashin tsaro – Atiku

Buhari da APC ne ya kamata su dauki alhakin rashin tsaro – Atiku

Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 23 ga watan Afrilu, Alhaji Atiku Abubakar, ya fada ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da su dauki alhakin matsalar rashin tsaro a kasar.

Atiku na martani ne ga wani rahoto da kungiya mai zaman kanta da ke zama a Amurka ta saki, wacce ake kira da cibiyar diflomasiyya da damokradiyya wato “Centre for Diplomacy and Democracy”.

A rahoton, kungiyar mai zaman kanta tad aura laifin adawa a Najeriya akan dalilin kasha-kashe, sace-sacen mutane, zubar jini da ayyukan ta’addanci a fadin kasar.

Buhari da APC ne ya kamata su dauki alhakin rashin tsaro – Atiku
Buhari da APC ne ya kamata su dauki alhakin rashin tsaro – Atiku
Source: Depositphotos

Sai dai, a wani jawabi a ranar Talata, 7 ga watan Mayu daga hadimin Atiku, Mista Paul Ibe, tsohon mataimakin Shugaban kasar ya bayyana rahoton a matsayin kirkirarren rubutu daga kagaggen kungiya mai zaman kanta.

Atiu yace hakan nuni ne ga yadda gwamnatin ta dukufa wajen zurfafa rabuwa da habbaka rashin daidaituwa a Kasar.

KU KARANTA KUMA: An sa ranar da za ayi shari’ar ruguje takarar Shugaba Buhari da Atiku

Dan takarar Shugaban kasar na PDP yace abun bankyama ne yadda gwamnatin Buhari abubuwanta, maimakon yin aiki da hankali wajen amincewa duniy cewa manufofinta da ayyukanta ne suka haddasa rabuwa a kasar.

Ya caccaki Shugaban kasar da tawagarsa akan zabar aiki da kungiya mai zaman kanta wacce bata da alkibla don tad aura laifinta akan yan adawa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel