Mutane 5 sun mutu a sanadiyyar harin yan bindiga a jahar Taraba

Mutane 5 sun mutu a sanadiyyar harin yan bindiga a jahar Taraba

Wasu gungun yan bindiga sun kai hare hare a kauyen Murbai dake cikin karamar hukumar Ardo Kola ta jahar Taraba inda suka kashe mutane biyar, tare da fatattakar al’ummar kauye da dama, inda a yanzu haka suka zama yan gudun hijira.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kaddamar da hare haren ne a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu a kauyen Yowai dake cikin karamar hukumar Jalingo, daga nan suka shiga kauyen Yelwa dake cikin garin Abare na karamar hukumar Ardo Kola a ranar Talata.

KU KARANTA: Ina sane da nauyin dake kaina, kuma ina sane da abinda nake yi sarai – Shugaba Buhari

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan sun shiga garuruwan ne akan babura dauke da muggan makamai, inda shigarsu keda wuya suka kaddamar da harbin mai kan uwa da wabi wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyar nan take, sa’annan suka kona gidaje da dama.

Guda daga cikin wadanda abin ya faru a gabansu, Francis Nomiri ya bayyana cewa mahaifinsa na daya daga cikin mutanen da suka jikkata a sanadiyyar harin sakamakon harbin bindiga daya kuskureshi.

Sai dai kwamishinan Yansandan jahar, Alkassim Sanusi ya tabbatar da aukuwar harin, amma yace tuni sun aika da jami’an tsaro zuwa yankin domin kwantar da hankulan jama’an tare da basu kariya da dukiyoyinsu.

Daga karshe, kwamishina Sanusu yace sun kaddamar da bincike akan lamarin don gano wadanda keda hannu cikin shiryawa tare da aiwatar da hare haren da nufin kamasu da kuma hukuntasu kamar yadda doka ta tanada.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel