An sa ranar da za ayi shari’ar ruguje takarar Shugaba Buhari da Atiku

An sa ranar da za ayi shari’ar ruguje takarar Shugaba Buhari da Atiku

Mun samu labari cewa za a zauna a babban kotun tarayya da ke Abuja a karshen Watan gobe saboda sauraron karar da ake yi a game da kudin da Atiku Abubakar da shugaba Muhammadu Buhari su ka kashe a lokacin zaben 2019.

Wani ‘Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NRM a zaben bana, Usman Alhaji, shi ne ya shigar da kara kotu inda yake so a soke takarar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma shugaba Muhammadu Buhari na APC.

Alhaji ya nemi kotu ta rushe takarar da manyan ‘yan siyasar su kayi a zaben 23 na Watan Fubrairun 2019, a bisa zargin cewa sun kashe kudin da ya haura Naira Biliyan 1 da hukumar zabe ta warewa masu neman takarar shugaban kasa.

KU KARANTA: An hada-kan Tinubu da Gwamnan APC da ake rigima kafin zabe

An sa ranar da za ayi shari’ar ruguje takarar Shugaba Buhari da Atiku

Kotu na zama a kan kudin da Buhari da Atiku su ka kashe a zaben 2019
Source: UGC

Ezekiel Ofou wanda shi ne Lauyan Usman Alhaji, ya fadawa kotu ta soke takaran na Atiku Abubakar da Muhammadu Buhari ne saboda sabawa sashe na 91(2) na dokokin zaben Najeriya da su kayi wajen yakin neman zaben bana.

Lauyoyin da ke kare shugaba Muhammadu Buhari da APC sun samu zuwa kotu a zaman da aka yi jiya Talata 7 ga Watan Mayu. Sai dai Lauyoyin hukumar INEC da kuma ‘dan takarar babbar jam’iyyar hamayya na PDP ba su samu zuwa ba.

Ofou ya nemi a sa rana a cigaba da shari’a ganin cewa Kotu ta sanar da duk wanda ake tuhuma, kuma ana ta bata lokaci wajen dage shari’ar. Lauyan APC bai yi gardama ba, wanda hakan ya sa kotu tace za a zauna ayi hukunci a Ranar 27 na Yuni.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel