Ramadana: Coci ta yiwa al'ummar musulmi rabon hatsi a Kaduna

Ramadana: Coci ta yiwa al'ummar musulmi rabon hatsi a Kaduna

- Wata Coci mai suna Christ Evangelical and Life Ministry ta rabawa wasu al'ummar jihar Kaduna hatsi da kayan masarufi albarkacin watan Ramadana

- Wannan dai shine karo na hudu da cocin ke bayar da irin wannan talafin ga masu bukata ta musamman, 'yan sansanin gudun hijira, gidan marayu da gidajen kurkuku a Kaduna

- Faston cocin, Yohanna Buru ya ce yana aikata haka ne domin karfafa dangata mai kyau da zaman lafiya tsakanin addinai a Kaduna

Ramadana: Coci ta yiwa al'ummar musulmi rabon hatsi a Kaduna

Ramadana: Coci ta yiwa al'ummar musulmi rabon hatsi a Kaduna
Source: Twitter

Shugaban cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Fastor Yohanna Buru ya fara rabbon kayayakin abinci ga al'ummar musulmi a wasu sassan jihar Kaduna domin tallafa musu yayin azumin watan Ramadana.

"Wannan shine karo na hudu da cocin ke rabon buhunnan hatsi da sauran a sansanin 'yan gudun hijira, gidajen kurkuku, gidajen marayu da ma al'umma da ke bara a kan tituna.

"Muna aikata hakan ne domin karfafa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban domin a zauna lafiya kamar yadda litaffan mu masu tsarki suka koyar.

DUBA WANNAN: Kotu ta umurci matar aure ta mayarwa mijinta sadakin N500 da ya biya

"Ya dace mu tuna cewa Allah daya muke bautawa kuma dukkan mu daga Adamu da Hauwa'u muka fito, saboda haka ya zama dole mu hada hannu mu tallafawa juna," inji shi.

Faston ya kuma yi kira ga masu hannu da shunu musulmi su rika tunawa da wadanda ba su da hali, wadanda ke sansanin 'yan gudun hijira da wadanda mazajen su suka mutu a unguwannin su domin saukaka musu yin azumi a watan Ramadan.

A yayin da ya ke taya al'ummar musulmi murnar zuwa watan Ramadana, ya yi kira ga limamai da malamai su cigaba da addu'ar samun zaman lafiya da hadin kai a Najeriya.

A bangarensa, Shugaban kungiyar mutane masu bukata ta musamman, Mallam Abdullahi Samai'la ya mika godiyarsa ga cocin bisa wannan gudunmawa da ta bawa al'umma musamman a wannan wata mai albarka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel