LOOM: Masu zamba cikin aminci su na samun karbuwa wajen ‘Yan Najeriya

LOOM: Masu zamba cikin aminci su na samun karbuwa wajen ‘Yan Najeriya

- Bayan rushewar tsarin nan na MMM, an sake kawo wani sabon salo Najeriya

- Wani sabon shiri na LOOM yana samun karbuwa ta yanar gizo a halin yanzu

- Jama’a ba su dandara da abin da ya faru da tsarin MMM a shekarar 2017 ba

Asarar makudan kudin da aka yi a tsarin MMM bai isa mutane da-dama daukar darasi ba, bayan da yanzu aka sake shigo da wani makamancin wannan tsari wanda ya lashewa ‘Yan Najeriya makudan miliyoyi a shekarun baya.

Bisa dukkan alamu ‘Yan Najeriya ba su dandara da asarar kudi wajen damfara ba inda su ke shiga cikin wannan sabon tafiya mai suna LOOM. A wannan shiri na LOOM, mutum ya kan samu shiga ne ta manhajar WhatsaApp.

KU KARANTA: Za ta biya Mijin ta sadakin da ya kashe wajen auren ta

Wadanda su ke kan wannan tsari za su sa kudi N1, 000 ko N2, 000 har zuwa N13, 000 da nufin cewa za a ribanya masu kudin na su har sau 8 muddin mutum ya kawo wani sabon-shiga. Wannan tsari ya zo ne cikin matakai har 4.

Akwai nau’o’i na LOOM wanda su ka hada da Purple, Blue, Orange da kuma Red. Idan mutum yayi nisa a wannan tsari, launin matsayinsa zai rika canzawa. A haka dai jama’a su ke samun kazamar riba ba tare da aikin far ko baki ba.

Wanda ya sa N1,000, zai samu N8,000; Wanda kuma ya zuba N2,000, zai tashi da N16,000; sannan kuma wanda ya sa N13,000, zai samu har N104,000. Sai dai a karshe irin wannan tsari ya kan rushe bayan an tara makudan kudin jama’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel