Tabarbarewar tsaro: Gwamnati bata baiwa kungiyar Miyetti Allah N100bn ba

Tabarbarewar tsaro: Gwamnati bata baiwa kungiyar Miyetti Allah N100bn ba

-Mohammed Adamu ya karyata zargin da ake yiwa gwamnatin tarayya akan ta baiwa kungiyar Miyetti Allah N100bn

-Mukaddashin sufeton yan sanda yayi ganawar sirri da yan majalisar dattawa ta tsawon sama da awa biyu

Mukaddashin sufeton yan sanda, Mohammed Adamu ya karyata zance dake yawo a halin yanzu na cewa gwamnatin tarayya ta baiwa kungiyar Miyetti Allah kudi N100bn domin kawo karshen garkuwa da mutane dake addabar kasar nan.

Adamu yayi wannan furucin ne yayinda yake tattaunawa da yan jarida jim kadan bayan ya fito daga wata ganawa ta sirri tsakanin shi da majalisar dattawa wacce aka dauki sama da sa’o’i biyu kan a gama.

Tabarbarewar tsaro: Gwamnati bata baiwa kungiyar Miyetti Allah N100bn ba

IG Mohammed Adamu
Source: Original

KARANTA WANNAN:Kotun daukaka kara ta baiwa Modibbo nasara a zaben majalisar dokoki

Biyo bayan wannan labarin dake yawo a kafofin sadarwa, kungiyar rubuce-rubuce kan kare hakkin bil adama ta Najeriya ta nuna rashin jin dadinta akan wannan lamari. Inda take ganin sam bai kamata ace gwamnatin tarayya ta dauki kudi N100b ta baiwa kungiyar Miyetti Allah ba.

Sufeton na yan sanda yace, bukatar yin hakan ma bata taso ba, idan har ana so a kawo karshen garkuwa da mutane a kasar nan. Zance dake yawo a kafofin sadarwa shaci fadine kawai sam ba magana ba ce mai tushe.

Yayinda ake tambayarsa akan zargin jami’an yan sanda da yiwa wasu karuwai fyade a Abuja, sufeton ya tabbatar mana da cewa an riga da an kafa kwamiti domin binciken gaskiyar lamarin. Duk jami’in da aka same shi da laifi tabbas zai fuskanci hukunci mafi dacewa dashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel