Abin kunya: An kaure da dambe a zauren majalisa, an karairaya sandan iko

Abin kunya: An kaure da dambe a zauren majalisa, an karairaya sandan iko

Rikici ya barke zauren majalisar dokokin jahar Jigawa a ranar Talata, 7 ga watan Mayu tsakanin yayan majaisar wanda har ta kai ga sun karairaya sandan ikon majalisar gida uku, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Legit.ng ta ruwaito wannan rikici ya samo sila ne yayin da kaakakin majalisar ya bayyana kudurin yin kwaskwarima ga dokar hana duk wani tsohon kaakakin majalisa ko mataimakinsa da aka taba dakatarwa ko tsigewa daga sake neman mukamin kaakaki da mataimakin kaakaki.

KU KARANTA; Karamar magana ta zama babba: Batun raba masarautar Kano gida 4 ta samu tagomashi

Furta wannan batu keda wuya sai kawunan yan majalisar ta rabu biyu, yayin da wani bangare ke goyon bayan kudurin, bangare guda kuma ke nuna adawa da kudurin a karkashin jagorancin Abdulrahman Alkassima dake wakiltar mazabar Yan kwashi.

Ga bidiyon rikicin kamar yadda jaridar Premium Times ta daukoshi.

Shi dai dan majalisa Alkassim shine akan gaba wajen kokarin hada kan yan majalisar don ganin sun mayar da tsohon kaakakin majalisar Idris Jahun mukaminsa, sai dai kimanin shekaru uku da suka gabata ne yan majalisar suka tsige Jahun a matsayin kaakaki, don haka kaakakin majalisar mai ci ya nuna rashin amincewarsa da komawa mukamin.

Kafin a ankara fada ya kaure tsakanin bangarorin biyu, inda suka cusa ma junansu hannu, ana cikin haka ne sai wasu yan majalisa daga bangarorin biyu suka tunkari sandan ikon majalisar, wancan na ja wancan na ja har sai da suka yi masa gunduwa gunduwa.

Da kyar da sudin goshi aka shawo kan yan majalisar, har hankula suka kwanta, amma a yayin da ake wannan karakaina, an fatattaki yan jaridu da ma’aikatan majalisar, sa’annan yansandan kwantar da tarzoma sun bazama a farfajiyar majalisar, daga karshe aka rufe majalisar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel