Hisbah na bukatar garambawul - Ganduje

Hisbah na bukatar garambawul - Ganduje

Gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa hukumar Hisbah dake jihar ta bace hanya, saboda haka hukumar tana bukatar a gabatar da gyare-gyare a kanta

Gwamnan jihar, wanda ya yi jawabin a wurin wani daurin auren zawarawa da ya shirya a jihar karshen makon nan da ya gabata, gwamnan ya bayyana cewa hukumar tana taka muhimmiyar rawa wajen rage mutuwar aure a fadin jihar, sai dai gwamnan ya ce hukumar ta na bukatar a gabatar da gyare-gyare a kanta.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ita ce aka dorawa alhakin tantance duk wani auren zawarawa, da kuma shirya bikin auren wanda gwamnatin jihar take gabatar lokuta da dama a fadin jihar.

Hisbah na bukatar garambawul - Ganduje
Hisbah na bukatar garambawul - Ganduje
Source: UGC

A wannan karon gwamnatin jihar ta aurar da zawarawa kimanin dubu uku, inda hukumar ta bayyana cewa sai da ta binciki lafiyarsu sosai kafin ta daura musu auren.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta biya kudi kimanin naira miliyan talatin a matsayin sadaki ga ma'auratan.

Da yake jawabi jim kadan bayan kammala daurin auren, gwamnan jihar ya bayyana ce hukumar yanzu ta lalace inda siyasa da kuma rashin gaskiya ya yi katutu a cikinta.

KU KARANATA: Kano: Shugaban majalisa da mataimakinsa zasu samu fansho da alawus na tsawon rayuwa

Sai dai a wannan karon an gabatar da bikin ba tare da shugaban hukumar ba wato Malam Ibrahim Daurawa, wanda ya ke shugabantar hukumar na kusan shekaru goma.

An yi ta samun rade-radi daga mutane da ke nuna cewa an kori Malamin daga mukaminsa. Amma har ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ke nuni da cewa an kori Malamin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel