Hukumar NUC ta amince a kafa Jami’o’i a cikin Jihar Imo

Hukumar NUC ta amince a kafa Jami’o’i a cikin Jihar Imo

Hukumar NUC mai kula da jami’o’in Najeriya ta amince a bude wasu Jami’o’i 3 a Jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya. Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta rahoto wannan a makon nan.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnati Najeriya ta amince a bude wasu sababbin Jami’o’i a Imo a cikin ‘yan kwanakin nan. Wannan na nufin jihar za ta samu Jami’o’i har 6 ita kadai idan komai ya tabbata.

Sababbin Makarantun da za a bude su ne: Jami’ar fasaha da kirkire-kirkire da ke Garin Omuma, Jami’ar kiwon lafiya da za a bude a Ogboko, da kuma wata Jami’ar kimiyya a cikin Garin Onuimo.

Shugaban hukumar NUC na kasa, Farfesa Abubakar Rasheed, yayi jawabi a jiya Talata 7 ga Watan Mayu bayan ya gana da gwamnan na jihar Imo, Rochas Okorocha a game da wannan shiri da yake yi.

Abubakar Rasheed, ya bayyana cewa wadannan sababbin makarantu har 3 sun cika duk wasu sharudodin NUC da ake bukata wajen kafa jami’a a kasar, don haka aka gwamnati ta amince a kafa su.

KU KARANTA: Kasashen da su ka fi karfin arziki a fadin Duniya

Hukumar NUC ta amince a kafa Jami’o’i a cikin Jihar Imo

Jihar Imo za ta samu manyan Jami’o’i 6 ita kadai
Source: UGC

NUC ta amince da jami’o’in ne bayan majalisar dokokin jihar Imo ta sa hannu wajen kafa su. Farfesa Rasheed ya kuma kara da cewa hukumar za ta ba wannan jami’o’i satifiket tun a jiya Talata.

Shugaban na NUC ya kuma fadawa manema labarai cewa daga cikin shirin wannan gwamnati shi ne dagewa wajen ganin yawan jami’o’in da ake da su sun kara yawa, saboda masu neman ilmi.

A jawabin na Farfesa Abubakar Rasheed, yace ana yawan samun masu bukatar shiga jami’a a cikin shekarun nan, amma babu isassun jami’o’in da sama da kashi 80% na Daliban za su je su yi karatu.

Gwamna Rochas Okorocha mai shirin barin gado ya nuna cewa zai yi bakin-kokarinsa na ganin wadannan sababbin makarantu ba su rasa kudin shiga domin gudanar da harkokin jami’ar ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel