Tsaro: Buhari ya rantsar da wani kwamitin mutum 14 domin inganta tsaron cikin gida

Tsaro: Buhari ya rantsar da wani kwamitin mutum 14 domin inganta tsaron cikin gida

A ranar Talata ne gwamnatin tarayya ta rantsar da wani kwamitin mutum 14 domin inganta tsaron cikin gida da fitar da taswirar kirkirar 'yan sandan jihohi.

Wannan na zuwa ne sati guda bayan mukaddashin babban sifeton 'yan sanda na kasa (IGP), Mohammed Adamu, ya sanar da cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi umarnin fara tunanin kaddamar da 'yan sandan jihohi a fadin kasar nan.

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Gida Mustapha, ne ya rantsar da kwamitin a ofishinsa. Ya bayyana cewar shugaba Buhari ya bayar da umarni ga manyan ma'aikata dake karbar horo a makarantar NIPSS dake Kuru a jihar Filato da su yi nazari a kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Ana sa ran kwamitin da Dakta Amina Shamaki ke jagoranta zai mika rahoton aikin da aka bashi a cikin sati biyu masu zuwa.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar wasu kungiyoyi biyu dake rajin tabbatar da mulki nagari a Najeriya, CD da CACOL sun ce matukar gwamnatin tarayya ta bar harkokin tsaro a yankin arewa maso yamma suka cigaba da tabarbarewa, babu shakka nan ba da dadewa ba 'yan bindiga zasu kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari hari ko kuma ma su sace shi.

Kungiyoyin biyu sun bayyana hakan ne a wata hira daban-daban da jaridar Punch tayi da su.

Shugaban kungiyar CD na kasa, Usman Abdul, ya ce, "bari na fada muku, da a ce shugaba Buhari ya na garin Daura ranar da 'yan bindiga suka kai hari, zasu iya sace shi."

A nasa bangaren, babban darektan kungiyar CACOL, Debo Adeniran, ya ce, "rashin kwarewa wajen iya tattara bayanan sirri ne ya jawo aka kai hari Daura. Da a ce jami'an tsaro sun bi hanyar da ta dace wajen samun bayanan sirri, da hakan ba ta faru ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel