Zaben gwamnan Kano: Kotu bata amince PDP ta yi wa takardun zaben binciken kwa-kwaf ba

Zaben gwamnan Kano: Kotu bata amince PDP ta yi wa takardun zaben binciken kwa-kwaf ba

A hukuncin da kotun dake sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta yanke a yau Talata, Kotun bata amincewa jam’iyyar PDP ta yi binciken kwa-kwaf ba kamar yadda ta nema a gaban kotun.

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa a zaman da kotun sauraren korafin zaben gwamnan jihar Kano tayi a ranar Talata, 7 ga watan Mayu, ta zartar da hukunci, inda ta nuna rashin amincewa da bukatar PDP na yi wa takardun zaben biciken kwa-kwaf.

Mai shari’a a kotun, Halima Shamaki ta ce dokar zabe bata amince da ayi wa takardun zabe binciken kwa-kwaf ba sai dai za a iya bin takardun da aka rubuta sakamakon zaben wanda aka yiwa kwafi a dudduba.

Zaben gwamnan Kano: Kotu bata amince PDP ta yi wa takardun zaben binciken kwa-kwaf ba

Zaben gwamnan Kano: Kotu bata amince PDP ta yi wa takardun zaben binciken kwa-kwaf ba
Source: UGC

Tun farko dama lauyan jam’iyyar PDP Maliki Kuliya-Umar ne ya roki kotu da ta amince wa jam’iyyar ta gudanar da irin wannan bincike.

Shi kuwa lauyan jam’iyyar APC, Aliyu Umar ya ce bai dace kotu ta ba wani irin wannan dama ganin cewa hakan ya saba wa dokar hukumar Zabe da kasa.

KU KARANTA KUMA: Kano: Shugaban majalisa da mataimakinsa zasu samu fansho da alawus na tsawon rayuwa

Ita kanta hukumar Zabe ta ki amincewa da wannan dama da PDP ta nema a kotu.

Akarshe kotu ta ba jam’iyyar PDP din dama ta bincike takardun wadanda suke an riga an yi kwafin su domin ci gaba da shari’ar sannan su tsayar da lokacin da za agama dube-duben a dawo kan shari’ar tsangwararanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel