Juyin mulki aka yi a zaben 2019 ba komai ba inji Gwamna Wike

Juyin mulki aka yi a zaben 2019 ba komai ba inji Gwamna Wike

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana abin da Rundunar Sojojin Najeriya su kayi a jiharsa a lokacin zaben 2019 da juyin-mulki. Gwamnan yayi wannan jawabi ne a gaban wasu ‘Yan majalisa jiya.

Nyesom Wike yake cewa Sojojin Najeriya sun yi kokarin ganin sun kakaba wasu shugabanni na-dabam a zaben da aka yi bana a Jihar Ribas, inda yace ba a taba samun Sojojin da su ka bata sunan su a Najeriya kamar na yanzu ba.

Mai girma gwamna Wike yayi wannan bayani ne a jiya Litinin 6 ga Watan Mayu a gaban wasu ‘yan kwamitin tsaro da shari’a da kare hakkin Bil Adama na majalisar wakilan tarayya da su ka kawo masa ziyara a gidan gwamnati.

Gwamnan yace abin takaici ne yadda Sojoji su ka rika sabawa doka don kurum cin ma burin siyasa. Wike ya zargi Dakarun Soji da kashe mutanen Ribas a lokacin da ake zabe a jihar. Wike yace ba a taba jin irin wannan abu a tarihi ba.

KU KARANTA: Gwamnan APC yace akwai masu iya kawowa Buhari cikas kafin 2023

Juyin mulki aka yi a zaben 2019 ba komai ba inji Gwamna Wike
Gwamnan Ribas ya zargi Sojojin Najeriya da hada-kai da Gwamnatin Tarayya
Source: UGC

Nyesom Wike yake fadawa ‘yan majalisar cewa kowa ya san cewa hambarar da gwamnatin PDP aka yi yunkurin yi a zaben bana. Ko da gwamnan bai kira suna ba, ya bayyana cewa an yi kokarin ganin wasu sun yi nasara da karfin tsiya.

Gwamnan na PDP ya bayyana yadda jami’an F-SARS su ka hallaka wani kwararren ‘Dan Boko kuma babban Akanta domin kurum a murde zabe. Haka zalika Gwamnan ya zargi babban GOC na Soji da hada-kai da wasu ‘Yan siyasa.

Wike yace gwamnatin Buhari ba ta taba taimaka masa wajen yaki da rashin tsaro a jihar ba amma aka nemi ayi amfani da Soji wajen murde zaben Ribas da ya gabata. Gwamnan yace ya rasa gane farar hula ake ciki ko mulkin Soji a kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel