Yanzu-yanzu: Boko Haram sun can sun kai hari a Maiduguri

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun can sun kai hari a Maiduguri

Daruruwan al'umma suna tserewa daga gidanjen su sakamakon harin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai a halin yanzu a kusa da Maiduguri, babban birnin jihar a cewar mutanen garin Molai.

Sun iso da yawa zuwa unguwar Molai da ke kewayen garin Maiduguri.

A cewar wani mazaunin garin mai suna Ali Umaru, 'yan ta'addan sun kai hari a kan al'ummar garin ne jim kadan bayan sun sha ruwa.

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun can sun kai hari a Maiduguri

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun can sun kai hari a Maiduguri
Source: UGC

DUBA WANNAN: Yankin Kudu maso Gabas ne ya dace su fitar da shugaban kasa a 2023 - Balarabe Musa

Ali ya shaidawa Sahara Reporters a wayan tarho cewa, "Ina jin karar harbin bindiga daga wurare da yawa. Ba zan iya magana ba a yanzu, Boko Haram sun iso Molai a halin yanzu, kowa yana gudu."

Wata majiya daga jami'an tsaro ya ce jirgin yaki yana hanyarsa ta zuwa Molai domin takawa 'yan ta'addan birki.

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel