Kalubalantar sakamakon zabe: Za a fara sauraron karar Atiku a ranar Laraba

Kalubalantar sakamakon zabe: Za a fara sauraron karar Atiku a ranar Laraba

Kamar yadda jaridar The Punch ta samu tabbaci, kotun daukaka karar tare da karbar korafe-korafen zaben shugaban kasa, a ranar Laraba za ta fara sauraron karar dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan sanya Laraba domin fara sauraron karar zaben shugaban kasa na bana, kotun tun a ranar Talata ta ankarar da dukkanin masu ruwa da tsaki a kan korafi da suka hadar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC.

Kalubalantar sakamakon zabe: Za a fara sauraron karar Atiku a ranar Laraba

Kalubalantar sakamakon zabe: Za a fara sauraron karar Atiku a ranar Laraba
Source: Facebook

Sauran masu ruwa da tsaki da kotun ta ankarar da su ta hanayar lauyoyi masu wakilcin su sun hadar da; shugaban kasa Muhammadu Buharu tare da jam'iyyar sa ta APC da kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben bana, Atiku Abubakar.

Majiyar jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, manyan Alkalai biyar bisa jagorancin shugaban kotun daukaka kara na Najeruya, za su halarci zaman kotun wajen sauraron korafin Atiku da na jam'iyyar PDP.

KARANTA KUMA: Shugabanni ba za su samu kwanciyar hankali ba a jihar Zamfara - Gwamna Yari

Baya ga korafin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, kotun yayin zaman da za ta fara gudanarwa a ranar Laraba za ta saurari korafai uku na wasu jam'iyyu daban-daban tare da 'yan takarkarun su.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku na ci gaba da hawa kujerar naki ta rashin amincewa da nasarar shugaban kasa Buhari biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar tun a ranar 23 ga watan Fabrairu 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel