Kano: Shugaban majalisa da mataimakinsa zasu samu fansho da alawus na tsawon rayuwa

Kano: Shugaban majalisa da mataimakinsa zasu samu fansho da alawus na tsawon rayuwa

- Gwamnatin jihar Kano za ta sanya hannu akan wata doka da za ta bai wa duk wani kakakin majalisa da mataimakinsa damar karbar fansho da alawus na tsawon rayuwarsu

- Bayan haka kuma gwamnatin tace za ta dauki nauyin kula da dawainiyar lafiyarsu a ko ina a duniya

- Sannan gwamnatin za ta dinga siya musu ababen hawa bayan kowacce shekaru hadu

A yau Talatar nan ne gwamnatin jihar Kano ta sanya hannu akan wata doka da za ta ba wa kakakin majalisar jihar da mataimakinsa damar karbar fansho da alawus na tsawon rayuwarsu idan suka bar aiki.

Bayan fansho da alawus da za a basu, majiyarmu ta binciko cewa, kakakin majalisar da mataimakin na sa za a ba su damar fita kasar waje domin ganin likita a duk lokacin da ba su da lafiya, sannan gwamnatin jihar za ta dinga saya musu motoci bayan kowacce shekara hudu.

Kano: Shugaban majalisa da mataimakinsa zasu samu fansho da alawus na tsawon rayuwa

Kano: Shugaban majalisa da mataimakinsa zasu samu fansho da alawus na tsawon rayuwa
Source: Twitter

A tsarin bayar da fanshon, ya nuna cewa duk wani kakakin majalisa ko mataimakinsa da aka tsige shi daga ofis ba zai mori romon wannan tsari ba.

"Za a biya fanshon ne kawai ga kakakin majalisa da mataimakinsa, wanda suka gama aikinsu ba tare da sun samu matsalar tsigewa ba.

"Ga kakakin majalisa da mataimakinsa, wadanda suka bar ofis kafin lokacin su ya yi, in dai har ba tsige su aka yi ba, su ma za su mori romon wannan tsari.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An gurfanar da zababben gwamnan PDP a kotu

"Sannan kuma ga kakakin majalisa ko mataimakinsa da suka mutu akan mulki, su ma za a biya iyalansu fansho na tsawon shekarun da suka yi suna yin aiki.

"Gwamnatin jihar Kano za ta dinga sayawa kakakin majalisar da mataimakinsa sabbin ababen hawa duk bayan shekara hudu.

"Gwamnatin jihar kuma za ta dauki nauyin kula da lafiyar kakakin majalisar da mataimakinsa a gida Najeriya da kuma kasashen ketare idan bukatar hakan ta taso."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel