Azumi: Gwamnatin jihar Jigawa ta rage tsawon sa'o'in aiki

Azumi: Gwamnatin jihar Jigawa ta rage tsawon sa'o'in aiki

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da rage yawan sa'o'in aiki ga ma'aikatan gwamnatin jihar yayin azumin watan Ramadana na shekarar 2019.

Alhaji Isma'ail Ibrahim, kakakin shugaban ma'aikatan jihar Jigawa, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Dutse, kamar yadda kamfanin dillancin labarai (NAN) ya rawaito.

Ibrahim ya ce daga yanzu ma'aikatan gwamnati a jihar zasu ke zuwa wuraren aiki da misalin karfe 9:00 na safe sannan su tashi karfe 3:00 na rana, sabanin zuwa wurin aiki karfe 8:00 zuwa 5:00 na yamma, kamar yadda aka saba.

Azumi: Gwamnatin jihar Jigawa ta rage tsawon sa'o'in aiki

Gwamnan jihar Jigawa; Muhammed Badaru Abubakar
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa a ranakun Juma'a, ma'aika zasu fara aiki ne daga karfe 9:00 na safe, sannan su tashi karfe 1:00 na rana, sabanin karfe 3:00 da aka saba tashi daga aiki ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: Namu ya samu: Ta tabbata, Farfesa Tijjani Bande ya zama sabon shugaban majalisar wakilan UN

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar tayi hakan ne domin bawa ma'aikatan ta sukunin shan ruwa a tsanake da kuma yin aiyukan bauta da azumin ke zuwa da su.

"Muna fatan cewar ma'aikata zasu yi amfani da wannan lokaci mai albarka na watan Ramadana domin yiwa jihar Jigawa da kasa addu'ar samun zama lafiya da karuwar arziki," a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel