Shugabanni ba za su samu kwanciyar hankali ba a jihar Zamfara - Gwamna Yari

Shugabanni ba za su samu kwanciyar hankali ba a jihar Zamfara - Gwamna Yari

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Abubakar Yari, ya gargadi sabbin zababbun shugabannin kananan hukomomin jihar akan yiwuwar kara ta'azzarar barazana ta rashin tsaro da zamto alakakai a fadin jihar.

Gwamna Yari kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito cikin gargadi ya bayyana cewa, kalubale na rashin tsaro da ake fama a fadin jihar Zamfara zai tumfaya domin kuwa a halin yanzu wannan lamari somin tabi ne.

Gwamnan jihar Zamfara; Abdulaziz Abubakar Yari

Gwamnan jihar Zamfara; Abdulaziz Abubakar Yari
Source: Twitter

Yari ya bayyana hakan ne yayin bikin rantsar da sabbin shugabannin kananan hukomomi 14 na jihar da kuma nadin sabbin sakatarorin gwamnati na dindindin guda 14 da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Gusau.

Ya yi nuni da cewa, duba da yadda ta'addancin 'yan baranda, masu kashe-kashe da kuma masu garkuwa da mutane ke ci gaba da kaiwa wani munzali na halin ni 'ya su musamman cikin kauyukan jihar babu dare babu rana, ya ce shugabanni su zama cikin shiri na rashin samun kwanciyar hankali yayin riko da akalar jagoranci.

Gwamnan bayan taya murna ga sabbin shugabannin na kananan hukumomi, ya jingina nasarar su da yadda gwamnatin jam'iyyar APC ta samu karbuwa tare da shiga zukatan al'ummar jihar baki daya.

KARANTA KUMA: Ba rashawa ba ce matsalar mu, Najeriya ta rasa managartan shugabanni - Dogara

Ya yi gargadi a gare su da su kasance sun bi tafarki da duk wani tanadi da kundin tsarin mulkin Najeriya ya gindaya gwargwadon iko na mukaman su wajen inganta ci gaba da kuma jin dadin al'umma a jihar Zamfara.

Ya nemi sabbin shugabannin na kananan hukumomi da su kwatanta makamancin goyon baya da ya samu daga gare su zuwa ga sabon zababben gwamnan jihar, Alhaji Mukhtar Idris Kogunan Gusau.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel