Ba rashawa ba ce matsalar mu, Najeriya ta rasa managartan shugabanni - Dogara

Ba rashawa ba ce matsalar mu, Najeriya ta rasa managartan shugabanni - Dogara

Sabanin yadda ake ikirarin cewa rashawa ita ce ummul aba isin hana ruwa gudu a kasar nan, kakakin majalisar wakilai Honarabul Yakubu Dogara, ya ce rashin managartan shugabanni shi ne babban kalubale da ya zamto alakakai a Najeriya.

A ranar Talata cikin babban birnin kasar nan na tarayya, kakakin majalisar wakilai Honarabul Yakubu Dogara, ya ce rashin managarcin jagoranci shi ne ya zamto babban kalubale da ya dakile ci gaba a kasar nan sabanin yadda ake yiwa rashawa ikirari.

Kakakin majalisar wakilai Honarabul Yakubu Dogara

Kakakin majalisar wakilai Honarabul Yakubu Dogara
Source: UGC

Dogara ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin karawa juna sani da aka gudanar mai taken jagoranci, iko da kuma siyasar dimokuradiyya a Najeriya. Matasan zababbun shugabanni da dama sun halasci taron.

Kakakin Majalisar ya ce annoba da dama sun yiwa Najeriya dabaibayi na kalubalai da suka hadar da kasancewar ta mafi hatsarin kasa ta uku a duniya asakamakon yadda ta'addanci ya zamto ma ta karfen kafa, rashin aikin yi a tsakanin al'umma gami da gurbacewar kiwon lafiya.

Yayin kira na dattako da hangen nesa, Dogara ya nemi Matasan Najeriya musamman wadanda su ka samu shiga na riko da madafan iko a yayin babban zaben kasa na bana, da su mike tsaye wurjanjan wajen tabbatar da kyakkyawar makoma a kasar nan ta hanyar mangarcin wakilci.

KARANTA KUMA: Jihar Borno ta yiwa wasu jihohin Najeriya 6 zarra ta samun kudaden shiga

Kamar yadda jaridar Legit.ng ta hikaito daga bakin sa, Dogara ya ce babbar annoba da ta zamto alakakai a kasar nan ba ta wuce rashin magarcin jagoranci ba sabanin yadda ake ikirari cewa rashawa ita ce kan gaba wajen kasancewar ta tubalin hana ruwa gudu a Najeriya.

Duk da cewa rashawa na bayar da muhimmiyar gudunmuwa wajen dakile ci gaban kasar nan, Dogara ya ce rashin managartan shugabanni ya haddasa wannan mummunar annoba da kawowa yanzu ta ke haifar da duk wani durkuso da ake fama da shi Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel