Rundunar 'yan sanda ta haramta amfani da babur a jihar Adamawa

Rundunar 'yan sanda ta haramta amfani da babur a jihar Adamawa

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Adamawa ta sanar da cewar ta haramta amfani da babur a ilahirin fadin jihar da kewaye.

Rundunar ta sanar da hakan a cikin wani jawabi da kakakinta a jihar Adamawa, SP Othman Abubakar, ya fitar a ranar Talata, ya ce yin hakan ya zama wajibi ne biyo bayan amfani da 'yan ta'adda ke yi da babur wajen satar mutane da kai hare-hare yayin rikicin kabilanci.

Ya yi gargadin cewar rundunar zata fara fara fita sintirin kama duk wanda ta samu ya karya wannan doka.

"Rundunar 'yan sandan Adamawa na sanar da jama'a haramta amfani da babur a fadin jihar, mai yawan kananan hukumomi 21, har sai baba-ta-gani."

Rundunar 'yan sanda ta haramta amfani da babur a jihar Adamawa

'yan sanda
Source: Twitter

"Yin hakan ya zama wajibi ne saboda amfani da babur da 'yan ta'adda ke yi wajen gudanar da aiyukansu na ta'addanci da suka hada satar mutane, kai hare-hare yayin rikicin kabilanci da sauran miyagun laifuka.

DUBA WANNAN: Farfesa Tijjani Bande na daf da zama sabon shugaban majalisar wakilan UN

"Bayan wannan sanarwa, rundunar 'yan sanda zata fara sintirin kama masu kunnen kashi, da zasu ki yin biyayya ga wannan sabuwar doka," a cewar kakakin.

Rundunar ta bukaci jama'ar jihar su kasance masu bin doka tare da basu hadin kai a kokarin da suke yi na tsaron lafiyar su da dukiyoyinsu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar an taba haramta amfani da babur a jihar a shekarar 2014 bayan yawaitar kai hare-hare a sassan jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel