Matashi ya mutu a cikin rijiya a Kano

Matashi ya mutu a cikin rijiya a Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani matashi mai shekaru 15 a duniya da ya mutu a cikin wata rijiya a karamar hukumar Fagge na jihar.

Kakakin hukumar kashe gobarar, Alhaji Saidu Mohammed ne ya tabbatar da rasuwar matashin yayin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN a garin Kano a ranar Litinin.

Ya ce lamarin ya afku ne a ranar Litinin da yamma a gida mai lamba 295 a unguwar Gwagwarwa Quaters da ke jihar.

Matashi ya mutu a cikin rijiya a Kano

Matashi ya mutu a cikin rijiya a Kano
Source: Twitter

DUBA WANNAN: JAMB za ta fitar da sunayen fitattun 'yan siyasa da su kayi magudin jarabawa

Mohammed ya shaidawa NAN cewa hukumar kashe gobarar ta samu kiran neman dauki amma ko da jami'an su suka isa gidan sun tarar da gawan matashin ne a cikin rijiya.

"Wani Mai'unguwa Yakubu ne ya kira mu a waya misalin karfe 5:37 na yamma inda ya ce wani yaro ya fada rijiya.

"Bayan mun samu bayanin mun gaggauta tura jami'an mu masu bayar da taimako inda suka isa gidan misalin karfe 5:48," a cewarsa.

Jami'in ya ce ana gudanar da bincike domin gano musababbin rasuwar matashin.

"Mun tarar da gawarsa ne a rijiyar sannan daga bisani muka mika wa 'yan sanda gawar," inji Kakakin hukumar kashe gobarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel