Kotun daukaka kara ta baiwa Modibbo nasara a zaben majalisar dokoki

Kotun daukaka kara ta baiwa Modibbo nasara a zaben majalisar dokoki

-Kotun daukaka kara dake Yola ta tabbatar da Abdulrauf Modibbo a matsayin zababben dan majalisar dokoki mai wakiltar Yola ta arewa, kudu da kuma Girei

-Dalilin yin hakan ya biyo bayan dokar da aka saba yayin shigar da karar wacce ba'ayiba kan lokaci

Kotun daukaka kara sashen Yola ta tabbatar da Abdulrauf Modibbo na jam’iyar APC a matsayin zababben dan majalisa mai wakiltar Yola ta arewa/ Yola ta kudu da kuma Girein jihar Adamawa a majalisar dokokin kasa.

Hadakar alkalai uku ne ya bashi wannan nasara, inda alkalan suka hada da: Chidi Nwaoma, J.S Aribiyi da Abdullahi Bayero. Dukkanin alkalan sun hadu kan matsaya guda daya cewa an shigar da karar bayan kwanaki 14 da aka shata dominta sun kare.

Kotun daukaka kara ta tabbatar da Modibbo a matsayin wanda yayi nasara a zaben majalisar dokoki
Kotun daukaka kara ta tabbatar da Modibbo a matsayin wanda yayi nasara a zaben majalisar dokoki
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Siyasar Kaduna yanzu bata ubangida bace, inji El-Rufai

Da yake magana akan shari’ar lauyan Abdulrauf mai suna Samuel Atom yace badakalar ta samo asali tun a lokacin zaben fidda gwani na APC a watan Oktoba day a gabata inda wadansu yan jam’iyar suka nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben na fidda gwani suka kuwa zarce zuwa kotu domin yin kara.

“ Munyi iya bakin kokarinmu domin ganin anyi watsi da wannan karar tun farko, amma abin yaci tura sai gashi a yau kuma kotun daukaka karat a yanke hukunci mafi dacewa ta sallami karar.” Inji Atom.

Ya kara da cewa hukunci da wata karamar kotu ta yanke inda ta baiwa dan takarar PDP nasara wanda yake tunani zai mashi amfani a kotun daukaka kara, yau shima kotu tayi watsi dashi. Kotun daukaka kara tace, karamar kotun tayi kuskure yanke wannan hukunci.

Abokin aikin Atom mai suna Sule Shuaibu, yace “tabbas munyi farin ciki da wannan shari’a saboda karar an shigar da ita yayinda lokacinda aka shata na 14 domin shigar da ita ya riga ya shude, yin hakan kuwa ba laifi bane face tabbatar da bin yadda doka ta tsara.” A cewar Shuaibu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel