Annobar Yunwa na yiwa 'Yan Boko Haram dauki dai-dai - BMO

Annobar Yunwa na yiwa 'Yan Boko Haram dauki dai-dai - BMO

Kungiyar sadarwa ta shugaban kasa Muhammadu Buhari BMO, Buhari Media Organisation, ta ce annobar tsumangiyar kan hanya mai fyade mutum walau babba ko kuma karami, na yiwa mugiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram kisan mummuke.

Kungiyar BMO ta ce a halin yanzu masu tayar da kayar baya a yankunan Arewa maso Gabashin kasar nan sun dimauce tare da afkawa cikin halin ni 'ya su a sakamakon karancin kayan abinci da kayan more rayuwa na yau da kullum ya dabaibaye sansanan su.

Annobar Yunwa na yiwa 'Yan Boko Haram dauki dai-dai - BMO

Annobar Yunwa na yiwa 'Yan Boko Haram dauki dai-dai - BMO
Source: Twitter

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, kungiyar BMO ta fayyace hakan ne yayin watsi da rahoton cewa 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram na samu makudan kudi akalla Dalar Amurka 3,000 a kowace rana fiye da adadin kudi da dakarun sojin kasar ke samu.

Cikin wata sanarawa a garin Abuja da sa hannun jagoran kungiyar, Niyi Akinjinsu da kuma Sakataren ta, Cassidy Madueke, ta bayyana cewa halin kunci da tagayyara da mayakan Boko Haram suka tsinci kansu a halin yanzu na da babbar nasaba da kwazon rundunar dakarun sojin kasar nan yayin da ta sauya sabon salo na tunkarar ta'addanci.

KARANTA KUMA: Ganduje zai sauke dukkanin 'yan Majalisar gwamnatin sa, zai nada wadanda ba ya da shakkun biyayyar su a gare sa

Har ila yau kungiyar BMO na ci gaa da ikirarin cewa, rahotanni da ke fitowa daga filin daga a yankuna Arewa maso Gabashin Najeriya sun tabbatar da cewa mayakan Boko Haram na gab da zama tarihi a kasar nan.

A yayin ci gaba da yabawa kwazon dakarun sojin Najeriya, kungiyar BMO ta kuma yabawa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman tsayuwar dakan sa ta tsarkake duk wani nau'i na ta'addanci a fadin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel