Gwamnatin Jigawa ta rage sa’o’in aiki ga ma’aikatanta

Gwamnatin Jigawa ta rage sa’o’in aiki ga ma’aikatanta

-Ma'aikatan jihar Jigawa sun samu ragowar lokacin aiki saboda azumin Ramadana

-Gwamnan jihar ya bukaci ma'aikatan da sun sanya jiharsu cikin addu'o'insu na musamman a wannan wata mai albarka

Gwamnan Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar a jiya ya sanar da ragewar lokacin zuwa da kuma tashi daga aiki saboda azumin watan Ramadana.

Wannan sanarwar ta fitone daga ofishin shugaban ma’aiktan jihar wanda ya shaidawa jaridar Daily Trust.

Gwamnatin Jigawa ta rage sa’o’in aiki ga ma’aikatanta

Gwamna Badaru Abubakar
Source: Twitter

KU KARANTA:Yadda kotu zata yanke hukunci tsakanin Buhari da Atiku

Sanarwar ta bayyana cewa, ma’aikata a yanzu zasu rika zuwa aiki karfe 9 na safe su kuma tashi da karfe 3 na maraice daga ranakun Litinin zuwa Alhamis, sabin karfe 8 na safe zuwa 5 na maraice kamar yadda yake a da.

Ranar Juma’a kuwa, ma’aikatan zasu zo wuraren aikinsu da karfe 9 safe su tashi da karfe 1 na rana, sabanin karfe 8 na safe zuwa 3 na yamma.

“ Muna fatan ma’aikatan zasuyi amfani da damar kasancewa cikin watan Ramadana mai albarka domin yin addu’o’in neman kariya da kuma albarkar Allah ga jihar tasu.” Kamar yadda yazo cikin zance.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel