Buhari yayi juyayin rashin wata ‘yar siyasar dake matukar mara masa baya

Buhari yayi juyayin rashin wata ‘yar siyasar dake matukar mara masa baya

- Buhari yayi juyayin rashin wata ‘yar siyasar dake matukar mara masa baya

- “Za mu tuna da ita a matsayin daya daga cikin manyan magoya bayanmu,”

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana juyayinsa game da rasuwar Hajiya Hindu Ja’afaru Danmalam, wadda take mai matukar goyon bayan shugaban kasar ce tun farkon gwaggwarmayar siyasarsa.

Kamar yadda wata takardar bayanin da mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu ya raba ma manema labarai take cewa, shugaban kasa a cikin wani sakon da ya aika ma iyalan marigayiya Hindu Danmalam, da Sarkin Kano, da gwamnatin jihar Kano yace zai yi kewar Hjiya Hindu wadda tayi tsayin daka wurin kare shi da gwamnatinsa a duk lokacin bukatar hakan ta taso, koda kuwa a lokacin da ta hadu da tursasawar manyanta a gidan siyasa.

KU KARANTA: Yanzu- yanzu: Masu hada magungunna a Najeriya sun janye ayukkansu na tsawon awanni biyu

“Za mu tuna da ita a matsayin daya daga cikin manyan magoya bayanmu,” Shugaban kasa ya fada.

Ya roki Ubangiji Allah da ya gafarta ma marigayiyar.

Wata tawagar wakilai ce daga jihohin Kano da Jigawa a karkashin jagorancin Honorabul Farouk Adamu Aliyu tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai suka gabatar da sakon ta’aziyyar a madadin shugaban kasa.

Haka kuma, a kwanan baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da irin wannan sakon ta’aziiyar zuwa ga iyalai, da abokai da al’ummar kiristoci kan mutuwar Bishop Lanre Obembe,

Obembe wanda ya samar da cocin El Shaddai Bible Church dake Ikoyi Legas ya mutu ne yana da shekaru 63 bayan fama da wata rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

Shugaba Buhari ya aika da sakon ta’aziyyar ne ta hannun mai ba shi shawara ta musamman a sashen watsa labarai da wayar da kan al’umma

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Wanne minista ne ya kamata Buhari ya koma da shi a karo na biyu? | Legit TV

Source: Legit

Mailfire view pixel