Zaben 2020: Tinubu da Gwamna Akeredolu sun hadu sun sasanta a Abuja

Zaben 2020: Tinubu da Gwamna Akeredolu sun hadu sun sasanta a Abuja

Bisa dukkan alamu, an yi wata haduwa ta musamman inda aka yi zaman sulhu tsakanin gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da kuma babban jigon jam’iyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Tinubu.

A Ranar Lahadi 5 ga Watan Mayun nan ne Bola Tinubu ya zauna da Gwamna Rotimi Akeredolu domin shawo kan banbancin da ke tsakaninsu. An yi wannan zama ne a babban birnin tarayya Abuja domin fara shiryawa zaben 2020.

Rotimi Akeredolu ya fara tsayawa takarar gwamnan jihar Ondo ne a 2012 a karkashin jam’iyyar ACN kafin a kafa APC. Sai dai daga baya ya samu matsala da Jigon na APC, Bola Tinubu, wanda ya ki mara masa baya a zaben da ya ci.

KU KARANTA: Abin da ya sa rikicin cikin-gidan da ya barkowa APC a zaben bana inji El-Rufai

Bola Tinubu da mutanensa sun marawa Olusola Oke na jam’iyyar AD baya ne a zaben 2016, wanda a karshe Rotimi Akeredolu yayi nasara a APC. Yayin da ake shirin sabon zabe, wadannan manyan ‘yan siyasa sun fara shirin sulhu.

A zaben 2019, Tinubu yayi kokari wajen ganin APC ta hana na-kusa da gwamna Rotimi Akeredolu samun tikiti a jihar Ondo, wanda a karshen jam’iyyar ta APC ta sha kashi a zaben shugaban kasa da aka yi a hannun Atiku Abubakar na PDP.

Premium Times ta rahoto cewa an gana tsakanin Mai girma Akeredolu da Bola Tinubu ne bayan an samu labari cewa APC ta dakatar da gwamnan na ta. Ana zargin gwamnan na Ondo da shiryawa APC zagon-kasa a zaben da ya gabata.

KU KARANTA: Gwamnan Kano ya taso Sark Muhammadu Sanusi II a gaba

Wasu manyan APC su na ganin cewa Rotimi Akeredolu ya marawa wata jam’iyyar adawa baya ne a 2019. Yanzu duk wannan ya zo karshe bayan da gwamnan ya zagaya ya gana da Bola Tinubu ta sanadiyyar Jigon APC a Kudu Pius Akinyelure.

Pius Akinyelure ya dade yana so ya hada-kan ‘yan siyasar tun ba yau ba, sai kwanan nan ne hakan ya yiwu inda dukannin bangarorin su ka hadu a kan cewa lokaci yayi da za a hada-kai domin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben Yankin.

Hadimin gwamnan na jihar Ondo, Allen Sowore, ya tabbatar da wannan zama inda yace an kuma yi sulhu. Haka zalika Mai taimakawa tsohon gwamnan na Legas, Tunde Rahman ya tabbatar da zaman.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel