Babban sufeton yan sanda ya gargadi jami’ansa kan cin zarafin dan adam

Babban sufeton yan sanda ya gargadi jami’ansa kan cin zarafin dan adam

-Aikinmu baya goyon bayan cin zarafin dan adam don haka kowane jami'i sai ya kiyaye, inji Adamu Mohammed

-Sufeton yayi wannan gargadin ne a Inugu yayinda ake bude wani taron horo da karawa juna sani

Mukaddashin sufeton yan sanda yayi gargadi ga jami’an yan sanda akan sabawa dokokin kare hakkin bil adama. Yayi wannan gargadin ne yayinda da yake bude wani taron horar da jami'an yan sanda na kwana uku akan kare hakkin bil adama ranar Litinin a Inugu.

Bugu da kari, taron zai fadakar da jami’an akan sanin muhimmancin kula da hakkin dan adam yayinda jami’i ke gudanar da aikinshi. A don haka zai basu damar yin aiki cikin kwarewa da kuma sanin yakamata.

Babban sufeton yan sanda ya gargadi jami’ansa kan cin zarafin dan adam

Babban sufeton yan sanda ya gargadi jami’ansa kan cin zarafin dan adam
Source: UGC

KU KARANTA:Yadda kotu zata yanke hukunci tsakanin Buhari da Atiku

Ya ce “ Ko kadan hukumar yan sanda ba zata lamunta cin zarafi dan adam ba, duk wanda aka sameshi da laifin hakan kuwa zai fuskanci hukunci. Domin yin hakan tamkar cin mutuncin aikin yan sanda ne.

“ Wannan shine dalilin da yasa hukumar yan sanda ta shirya wannan taro domin koyar jami’anta sanin yadda yakamata a kiyaye hakkin dan adam. Wannan shiri dai ya shafi kowa da kowa daga cikin jami’an yan sanda, saboda idan har akwai mai wani tunani sai ya canza da wuri.”

Wadanda ke karbar horon sun fitone daga kwarrrun jami’ai masu fada da yan fashi, sashen yaki da ta’addanci na musamman da kuma tawagar babban sufeto kai har ma da sauransu.

Adamu wanda kwamishinan yan sanda mai kula da horon ya wakilta, Abiodun Odude, yace wannan horon yana daga cikin kudurinsu na sake shirya jami’an yan sandan ta yadda zasu samu amincewar yan Najeriya a fannin aikinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel