Babu sabon bincike kan Saraki - EFCC tayi karin haske

Babu sabon bincike kan Saraki - EFCC tayi karin haske

- Hukumar EFCC tayi karin haske akan batun bude sabon bincike kan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki

- Ta bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege

- Hukumar tace dama chan ana kan binciken mulkinsa na gwamnan jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) a jiya Litinin, 6 ga watan Mayu tayi watsi da rahoto akan gudanar da sabon bincike kan shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki.

Kakakin hukuman, Tony Orilade, a wani jawabi da ya saki a Abuja, yayi jawabi game da rahoto dake nuna cewa akwai sabbin bincike da ake gudanarwa akan shugaban majalisar a mulkinsa na gwamnan Kwara tsakanin 2003 da 2011.

Babu sabon bincike kan Saraki - EFCC tayi karin haske

Babu sabon bincike kan Saraki - EFCC tayi karin haske
Source: Depositphotos

Yayin da yake bayyana labarin a matsayin “kirkiran ganganci”, hukuman tayi nunin cewa ana farautan tsohon gwamnan ne a daidai lokacin sabon nadi na mukamin jakada da hukumar kae hakkin dan adam na kasa da kasa (IHRC) ta bashi kwanan nan alhalin kuwa ya kasance a karkashin bincike.

KU KARANTA KUMA: Gyaran dokar masarauta: An tsaurara tsaro a majalisar dokokin jihar Kano

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa babban Lauyan Najeriya, Mohammed Dele Belgore, wanda ke fuskantan zargin karkatar da kudi naira miliyan 450 gabannin zabukan 2015, a jiya Litinin ya sanar da wata babbar kotu da ke Legas cewa daga cikin kudaden ya baiwa kwamishinan yan sandan jihar Kwara a lokacin naira miliyan 10 wanda ya bayyana sunansa a matsayin Garba.

Hukumar EFFCC ta gufanar da shi a gaban babbar kotun da ke Legas bisa zargin amfana da naira miliyan 450 daga cikin dala miliyan 115.01, wanda tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison-Madueke, ta fitar akan harkar zaben 2015.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel