Kotu ta umurci matar aure ta mayarwa mijinta sadakin N500 da ya biya

Kotu ta umurci matar aure ta mayarwa mijinta sadakin N500 da ya biya

Wata kotun Shari'a mai daraja ta daya da ke zamanta a Magajin Gari Kaduna ta umurci wata mace mai shekaru 39, Esther Morris ta mayarwa tsohon mijinta, Tajudeen Musa mai shekaru 46 Naira 500 a kudin sadakinsa.

Alkalin kotun, Dahiru Lawal ya katse auren tsakanin mutanen biyu inda ya bukaci jami'an kotu su raka Morris zuwa gidan tsohon mijinta domin ta kwashe kayanta.

Morris da ke zaune a sabuwar barikin sojoji (NDA) da ke Afaka a Kaduna ce ta kai karar mijinta Musa inda ta bukaci a raba aurensu.

Kotu ta umurci amarya ta mayarwa ango sadakinsa N500
Kotu ta umurci amarya ta mayarwa ango sadakinsa N500
Source: Twitter

DUBA WANNAN: JAMB za ta fitar da sunayen fitattun 'yan siyasa da su kayi magudin jarabawa

"Munyi aure shekaru 11 da suka gabata. Allah bai bamu haihuwa ba.

"Tunda mu kayi aure, al'amurran rayuwarsa sun tabbarbare. Ya yi ikirarin ni da 'yan uwa na ne sanadiyar rashin samun haihuwarsa.

"Naira 500 ya biya a matsayin sadaki lokacin da zai aure ni. Ina son a raba auren mu. Ba zan iya cigaba da zama da shi ba," inji Morris.

Ta ce a kotu aka daura musu aure tun da farko.

"Halayen da ya ke nunawa sun bayyana cewa yana son a raba auren amma ya gaza tunkarar kotu domin a raba auren," a cewar Morris.

Wanda akayi kararsa a kotun, Tajudeen Musa, dan kasuwa da ke zaune a BZ 23 Abuja Road by Sardauna Crescent ya shaidawa kotu cewa shima yana goyon bayan a raba auren.

"Na aure ta tana kirista ne kuma bana son ta sake amfani da sunan mahaifi na, ta kuma dawo min da dukkan kayayakin da na mallaka a lokacin da na ke tare da ita."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel