Yanzu-yanzu: An gurfanar da zababben gwamnan PDP a kotu

Yanzu-yanzu: An gurfanar da zababben gwamnan PDP a kotu

- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta tisa keyar Sanata Ademola Adeleke, kuma zababben gwamnan jihar Osun a karkashin inuwar jam'iyyar PDP zuwa kotu

- Hukumar ta na zargin Sanatan da amfani da takardun bogi wurin lashe zabe

A jiya Litinin ne 6 ga watan Mayu, aka kama dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, inda yau Talata 7 ga watan Mayu aka mika shi gaban kotu.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya, 'yan sanda sun kama Sanata Adeleke da takardun karya.

Majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton cewa jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya sun kama Sanata Ademola Adeleke, zababben gwamnan gwamnan jihar Osun a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, a cewar kwamitin neman zaben shi, da kuma jam'iyyar shi.

Yanzu-yanzu: An gurfanar da zababben gwamnan PDP a kotu

Yanzu-yanzu: An gurfanar da zababben gwamnan PDP a kotu
Source: Twitter

Jam'iyyar da kwamitin na shi sun bayyana cewa, hukumar 'yan sandan Najeriya ta aikawa da Adeleke takardar gayyata, inda ya amsa kiran hukumar a babban ofishinta da ke Abuja, amma yana zuwa sai suka kama shi.

A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta nuna cewa Adeleke ya isa ofishin 'yan sandan da misalin karfe 9 na safe, kuma bai samu ganin jami'an 'yan sandan ba har sai da rana inda ake tuhumar sa da gabatar da takardun karya.

KU KARANTA: Satar mutane ita ce sabuwar sana'ar matasan Najeriya - Buhari

Daga nan aka wuce dashi ofishin 'yan sanda da ke Maitama da niyyar a kai shi kotu a yau Talata, 7 ga watan Mayu, sanarwar wacce ta bayyana cewa anyi niyyar a tozarta zababben gwamnan ne, saboda ganin ya ci zabe a jihar Osun ba tare da wata matsala ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel