Sakamakon jarabawa ta bogi: Kotu ta bayar da belin Sanata Adeleke

Sakamakon jarabawa ta bogi: Kotu ta bayar da belin Sanata Adeleke

Kotun Majisatare da ke zamanta a babban birnin tarayya, Abuja ta bayar da belin Sanata Adeleke a kan kudi Naira miliyan biyu bisa dalilan rashin lafiya domin ya tafi kasar Amurka ya ga likitocinsa.

An gurfanar da Mista Adeleke ne a ranar Talata bayan ya mika kansa ga jami'an 'yan sanda domin amsa tambayoyi a ranar Litinin.

'Yan sandan sun tuhume shi da aikata laifuka guda biyar masu alaka da kirkirar sakamakon jarabawa ta bogi.

A cewar tuhumar, Mr Adeleke ya gabatarwa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC takardun kammala karatu na bogi a shekarar 2017.

Sakamakon jarabawa ta bogi: Kotu ta bayar da belin Adeleke

Sakamakon jarabawa ta bogi: Kotu ta bayar da belin Adeleke
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: JAMB za ta fitar da sunayen fitattun 'yan siyasa da su kayi magudin jarabawa

Amma ya ki amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.

Bayan haka ne lauya mai kare shi ya bukaci kotu ta bayar da belin Adeleke.

Kotu ta amsa wannan rokon na lauyan inda alkalin kotun, Muhammed Zubairu ya bukaci a bayar da Naira Miliyan Biyu (N2 Million) da kuma mutum daya da zai karbe shi belin.

Ya ce dole wanda zai karbe shi belin ya kasance mazaunin Abuja kuma mai sana'a.

Kotun ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Yuni.

Mr Adeleke ya bar haraban kotun misalin karfe 12.22 na rana bayan ya kammala cika sharrudan belin.

An bashi damar fita kasar waje domin likitoci su duba lafiyarsa a ranar Litinin.

A cewar umurnin kotun tarayya na Abuja karkashin jagorancin Inyang Ekwo, an sa ran Mista Adeleke zai dawo Najeriya a ranar 9 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel