Gyaran dokar masarauta: An tsaurara tsaro a majalisar dokokin jihar Kano

Gyaran dokar masarauta: An tsaurara tsaro a majalisar dokokin jihar Kano

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a harabar majalisan dokokin jihar Kano a yau Talata, 6 ga watan Mayu.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an zuba jami'an tsaro a ciki da wajen majalisar inda suka kasance dauke da kayayyakin aiki.

Jami’an tsaron sun hada da yan sanda da Civil Defence a sashi daban-daban na harabar majalisan.

An tsayar da zirga-zirgan motoci a harabar majalisan yayin da jami’an tsaron suke duba motoci kafin basu damar shiga harabar.

An tsaurara matakan tsaro a majalisar dokokin jihar Kano yayinda yan majalisa ke shirin gyara dokar masarauta

An tsaurara matakan tsaro a majalisar dokokin jihar Kano yayinda yan majalisa ke shirin gyara dokar masarauta
Source: UGC

Har ila yau, a kofar shiga majalisan, wadanda aka tantance ne kadai ake baiwa daman shiga cikin majalisan.

KU KARANTA KUMA: Badakalar N450m: Na ba kwamishinan yan sandan N10m - Belgore

Kamar yanda majiyarmu ta Daily Trust ta gano, lamarin baya rasa nasaba da zaman majalisa na yau, inda ake sa ran kwamitin majalisar kan kananan hukuma da harkokin sarauta zata gabatar da rahotonta kan gyaran dokar masarauta na 1984.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin yin gutsun-gutsun da Masarautar kasar zuwa gidaje 4. Yanzu haka ana so a kirkiri wasu sababbin Sarakuna a Yankin Gaya, Karaye, Bichi da kuma kasar Rano.

Wani ‘dan majalisa, Salisu Ibrahim Chambers, shi ne ya fara kawo wannan kudiri a gaban zauren majalisar inda yake neman sauran Abokan aikinsa su amince da hakan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel