Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan bindiga a Zamfara, ta kashe 20

Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan bindiga a Zamfara, ta kashe 20

Rundunuar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta ce dakarunta na atisayen 'DIRAN MIKIYA' sun lalata sansanin wasu 'yan bindiga da wani kasurgumin dan ta'adda, Alhaji Lawal, ke shugabanta tare da kashe 20 daga cikin su a dajin Rugu dake jihar Zamfara.

Ibikunle Daramola, darektan yada labarai da hulda da jama'a na NAF, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabai da ya fitar a Abuja ranar Talata.

Daramola ya ce kai harin ya biyo bayan tabbatar da labaran sirri kan cewar kasurgumin dan ta'addar tare da dumbin mayakansa ya kafa wani sasani mai nisan kilomita 4 a yamma da jejin Rugu.

Ya ce a sanin ne Lawal ke ajiye da makamansa da ragowar kayan aikinsa da kuma shirya yadda za a kai hari a kan jami'an tsaro da farar hula.

"Bayan tabbatar da dukkan bayanan sirri da muka samu ta hanyar bincike da hikimar ISR, sai ATF ta aika jirgin yaki daya da wani jirgin mai saukar ungula suka kai hari sansanin.

Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan bindiga a Zamfara, ta kashe 20

Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan bindiga a Zamfara
Source: Twitter

"Jirgin mu na yaki (Alpha jet) ya yi ruwan wuta kai tsaye a sansanin, lamarin da ya jawo nan take wuta ta kama cin sansanin sakamakon kama wa da wuta da ma'adanar su ta man fetur tayi. Ragowar kayayyakinsu da suka hada da makamai, sinadarai masu fashe wa, rumfuna da sauran su, duk wuta ta kone su," a cewar sa.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta haramta amfani da babur a jihar Adamawa

Ya kara da cewa a kalla 'yan bindiga 20 sun rasa ransu a sharar sansani da jirgin yaki mai saukar ungulu ya yi a sansanin bayan luguden wutar da jirgin 'Alpha Jet' ya yi.

Kakakin ya ce rundunar NAF tare da hadin gwuiwar ragowar rundunonin soji da hukumomin tsaro, zasu cigaba da aikin kakkabe 'yan bindiga daga yankin arewa maso yamma da ma kasa bakidaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel