Ana ci gaba da ragargazar Buhari kan furucin da yayi game da tsaro

Ana ci gaba da ragargazar Buhari kan furucin da yayi game da tsaro

Al'umman Najeriya da dama sun je shafukan sada zumunta a yanar gizo, su na ta caccakar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan wani barkwanci da ya yi game da matsalar tsaro da ya addabi kasar Najeriya.

A ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu ne Buhari ya yi wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda barkwanci cewa ya ga duk ya rame, ya rage kiba, saboda matsalar tsaro a kasar.

Wani bidiyo da ake ta watsawa, an nuno Shugaba Buhari na hira da manema labarai bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya inda ya shafe kwanaki 10 a wani ziyarar sa kai.

An yi masa tambaya akan matsalar tsaro a fadin kasar nan, musamman yawaitar garkuwa da mutane.

Ana ci gaba da ragargazar Buhari kan furucin da yayi game da tsaro

Ana ci gaba da ragargazar Buhari kan furucin da yayi game da tsaro
Source: Twitter

Sai Buhari ya amsa da cewa, “babu wata hanyar da za a yi tunanin samu da ta fi wadda ake a kai yanzu wajen magance matsalar tsaro.”

Ya kuma kara da cewa, “Ai na ga har Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya rage kiba, saboda fuskantar kalubalen tsaro a kasar nan."

Nan da nan wadanda wannan barkwanci bai yi wa dadi ba, suka fara caccakar Shugaba Muhammadu Buhari a shafukan su na tweeter.

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin AAC, Sowore, ya rubuta cewa, ” Buhari fa ya saki layi. Wannan babbar katobara ce.”

KU KARANTA KUMA: Tsaro: Kwanan nan 'yan bindiga zasu kai wa Buhari farmaki - CACOL

Obey Ezekwesili kuwa cewa ta yi, “yanzu kisan jama’a shi ne zai zama abin barkwanci kuma? Wannan kamar wanka ne da jinainan jama’ar da ake kashewa.

“Kai ne Babban Kwamandan Askarawan Kasar nan. Amma wata rana ‘yan Najeriya za su kawo karshen wannan barkwancin.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel