Matattu sun kada kuri'a a kananan hukumomi 3 yayin zaben gwamna a Imo - Nwosu

Matattu sun kada kuri'a a kananan hukumomi 3 yayin zaben gwamna a Imo - Nwosu

Uguwamba Uche Nwosu, dan takarar gwamna na jam'iyyar Action Alliance (AA) a zaben gwamna da akayi a ranar 9 ga watan Maris a jihar Imo ya yi ikirarin cewa binciken kwa-kwaf da aka gudanar a kan kuri'un zabe ya nuna cewa daruruwan matattun mutane sun kada kuri'u a kananan hukumomin Aboh Mbaise, Ahiazu da Ezihitte.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, (INEC) ta sanar da cewa dan takarar jam'iyyar PDP, Emeka Ihedioha ne ya lashe zabe. Sai dai Nwosu ya ce binciken kwa-kwaf da ya gudanar ya nuna cewa sakamakon da INEC ta fitar ya banbanta da ainihin zaben da al'umma suka gudanar.

A baya bayan nan ne kotun sauraren kararrakin zabe ta bawa dan takarar gwamnan na jam'iyyar AA ikon duba kuri'u da sauran ababen da akayi amfani da su a zaben.

Matattu sun kada kuri'a a kananan hukumomi 3 yayin zaben gwamna a Imo - Nwosu

Matattu sun kada kuri'a a kananan hukumomi 3 yayin zaben gwamna a Imo - Nwosu
Source: UGC

DUBA WANNAN: Yankin Kudu maso Gabas ne ya dace su fitar da shugaban kasa a 2023 - Balarabe Musa

A yayin da ya ke magana da manema labarai a Owerri, Nwosu ya ce ya yi matukar mamakin irin yadda aka tafka magudi a zaben da ta gabata.

"Bayan an sanar da sakamakon zaben, na shaidawa magoya baya na cewa ba a gudanar da zabe a kananan hukumomi guda uku ba, sune: Mbaise-Aboh, Ahiazu da Ezinhitte.

"Na shaida musu cewa an canza sakamakon zaben domin a bawa Ihedioha nasara. Bayan an bamu damar bincika takardun zaben, mun gano cewa daruruwan mutane da suka rasu sun kada kuri'u a zaben.

"Muna da mutanen da suka fada mana cewa sun ga sunayen 'yan uwansu da suka dade da rasuwa a cikin jerin sunayen wadanda su kayi rajistan zabe kuma daga bisani sunyi zaben.

"Mun kuma gano cewa adadin masu zabe da bataren zabe ya fadi ya sha ban-ban da adadin da card reader ya bayyana musamman a kananan hukumomi uku," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel