IGP ya isa majalisar dokokin kasar, ya jero wa majalisar dattawa bayani kan tsaro a ganawar sirri

IGP ya isa majalisar dokokin kasar, ya jero wa majalisar dattawa bayani kan tsaro a ganawar sirri

A yanzu haka, Mukaddashin Sufeto Janar na yan sanda, Moammed Adamu na cikin zauren majalisar dattawa, inda yake koro wa yan majalisar tarayya jawabai akan halin da tsaron kasar ke ciki.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa Adamu ya fara ziyartan ofisin babban mai ba shugaban kasa shawara a harkokin majalisar dokoki (majalisar dattawa), Ita Enang.

Legit.ng ta tattaro cewa yan majalisar sun gayyaci IGP da farko sakamakon halin da tsaron kasar ke ciki. Wannan shine karo na farko da shugaban yan sanda mai ci ya gurfana a gaban majalisar dattawa tun 2014.

IGP ya isa majalisar dokokin kasar, ya jero wa majalisar dattawa bayani kan tsaro a ganawar sirri

IGP ya isa majalisar dokokin kasar, ya jero wa majalisar dattawa bayani kan tsaro a ganawar sirri
Source: UGC

Ku tuna cewa Legit.ng ta ruwaito cewa Inspekto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu ya janye tsarin rabe-raben aiki na rundunar yan sandan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Mutanen wani Kauye sun fito Gari sun tare Tawagar Mataimakin Shugaban kasa

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Wasu kungiyoyi biyu dake rajin tabbatar da mulki nagari a Najeriya, CD da CACOL sun ce matukar gwamnatin tarayya ta bar harkokin tsaro a yankin arewa maso yamma suka cigaba da tabarbarewa, babu shakka nan ba da dadewa ba 'yan bindiga zasu kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari hari ko kuma ma su sace shi.

Kungiyoyin biyu sun bayyana hakan ne a wata hira daban-daban da jaridar Punch tayi da su.

Shugaban kungiyar CD na kasa, Usman Abdul, ya ce, "bari na fada muku, da a ce shugaba Buhari ya na garin Daura ranar da 'yan bindiga suka kai hari, zasu iya sace shi."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel