Badakalar N450m: Na ba kwamishinan yan sandan N10m - Belgore

Badakalar N450m: Na ba kwamishinan yan sandan N10m - Belgore

Wani Babban Lauyan Najeriya, Mohammed Dele Belgore, wanda ke fuskantan zargin karkatar da kudi naira miliyan 450 gabannin zabukan 2015, a jiya Litinin ya sanar da wata babbar kotu da ke Legas cewa daga cikin kudaden ya baiwa kwamishinan yan sandan jihar Kwara a lokacin naira miliyan 10 wanda ya bayyana sunansa a matsayin Garba.

Hukumar EFFCC ta gufanar da shi a gaban babbar kotun da ke Legas bisa zargin amfana da naira miliyan 450 daga cikin dala miliyan 115.01, wanda tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison-Madueke, ta fitar akan harkar zaben 2015.

Hukumar EFCC tace Belgore, tare da tsohuwar ministan tsare-tsare na kasa, farfesa Abubakar Suleimen, a reshen wani banki da ke Illorin a ranar 26 ga watan Maris, 2015 don sa hannu da kuma karban kudi naira miliyan 450.

Badakalar N450m: Na ba kwamishinan yan sandan N10m - Belgore

Badakalar N450m: Na ba kwamishinan yan sandan N10m - Belgore
Source: UGC

Har ila yau, Belgore ya gaskanta gayyata da manajan bankin yayi masa a ranar 26 ga watan Maris, 2015 don karban kudi naira miliyan 450, yace amman ya karkare da barin bankin ba tare da kudin ba.

KU KARANTA KUMA: Mutanen wani Kauye sun fito Gari sun tare Tawagar Mataimakin Shugaban kasa

An zargi Belgore da Suleiman akan karban kudin ba tare da bin cibiyoyin kudi ba, wanda ya saba ma dokar karkatar da kudi.

Amman wadanda ake tuhuman sun musanta zarge zargen.

Justis Rilwan Aikawa ya daga karan zuwa ranar 15 ga watan Mayu don cigaba bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel