Tsaro: Kwanan nan 'yan bindiga zasu kai wa Buhari farmaki - CACOL

Tsaro: Kwanan nan 'yan bindiga zasu kai wa Buhari farmaki - CACOL

Wasu kungiyoyi biyu dake rajin tabbatar da mulki nagari a Najeriya, CD da CACOL sun ce matukar gwamnatin tarayya ta bar harkokin tsaro a yankin arewa maso yamma suka cigaba da tabarbarewa, babu shakka nan ba da dadewa ba 'yan bindiga zasu kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari hari ko kuma ma su sace shi.

Kungiyoyin biyu sun bayyana hakan ne a wata hira daban-daban da jaridar Punch tayi da su.

Shugaban kungiyar CD na kasa, Usman Abdul, ya ce, "bari na fada muku, da a ce shugaba Buhari ya na garin Daura ranar da 'yan bindiga suka kai hari, zasu iya sace shi.

"Daga cikin alkawuran da shugaban kasa ya yi lokacin yakin neman zabe akwai batun inganta tsaro a fadin kasa. Amma abin takaici, yanzu haka maganar nan da muke yi, surukin shugaban kasa yana hannun masu garkuwa da mutane, ita kuma fadar shugaban kasa ta shiga juyayin sace shi.

Tsaro: Kwanan nan 'yan bindiga zasu kai wa Buhari farmaki - CACOL

Buhari bayan dawowar sa Najeriya a ranar Lahadi
Source: Twitter

"Abin kunya ne a ce gwamnati ta gaza samar da tsaro ga 'yan kasa, wanda yin hakan shine dalili na farko da yasa aka kirkiri gwamnati. Kalaman Garba Shehu, kakakin shugaban kasa sun tabbatar mana cewar gwamnati ta gaza a bangaren tsaron lafiyar 'yan kasa da dukiyoyin su."

DUBA WANNAN: Hukumar kula da gidajen yari ta kori babban Ofisa saboda safarar kwayoyi

A nasa bangaren, babban darektan kungiyar CACOL, Debo Adeniran, ya ce, "rashin kwarewa wajen iya tattara bayanan sirri ne ya jawo aka kai hari Daura. Da a ce jami'an tsaro sun bi hanyar da ta dace wajen samun bayanan sirri, da hakan ba ta faru ba.

"Abinda na yarda da shine; 'yan bindigar na son tabbatar wa da duniya cewar da suna son kai wa shugaban kasa hari, da sun yi hakan. Shugaban kasa kan ziyarci garin Daura lokacin sallah da sauran su. Sakon da 'yan bindigar suka aika shine babu wanda ya tsira daga sharrin su. Akwai bukatar jami'an tsaro su canja dabarunsu na yaki da aiyukan ta'addanci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel