Da duminsa: 'Yan majalisar dattawa suna can suna ganawa da IGP Adamu

Da duminsa: 'Yan majalisar dattawa suna can suna ganawa da IGP Adamu

Majalisar Dattawa ta gayyaci Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu zuwa zaurenta domin ya yi musu bayyani a kan halin tsaro a sassan Najeriya.

Ganawarsu da shugaban 'yan sandan na Najeriya ne abin farko da majalisar za ta fara aikatawa a yau Talata 7 ga watan Mayu.

Majalisar ta yanke shawarar ganawa da shugaban 'yan sandan a cikin sirri.

Da duminsa: 'Yan majalisar dattawa suna can suna ganawa da IGP Adamu

Da duminsa: 'Yan majalisar dattawa suna can suna ganawa da IGP Adamu
Source: Original

DUBA WANNAN: MTN ta bawa Sarki Sanusi II babban mukami

Sufeta Janar Mohammed Adamu ya bayyana a gaban majalisar ne sakamakon sakon da majalisar ta aike masa a makon da ya gabata a kan halin rashin tsaro a Najeriya da ya hada da yawaitan garkuwa da mutane, hare-haren 'yan bindiga da sauransu a sassan kasar.

Majalisar ta aike wasikar gayyatan ne ga Adamu sakamakon kudirin da Sanata Shehu Sani ya gabatar na janyo hankalin majalisar a kan kisar wani dan kasar Ingila da sace wasu uku da 'yan bindiga su kayi a wani gidan shakatawa da ke Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel