Dole a takawa ‘Yan bindiga burki kafin su shigo Abuja – Shehu Sani

Dole a takawa ‘Yan bindiga burki kafin su shigo Abuja – Shehu Sani

- ‘Yan bindigan da ke cikin Zamfara sun tsere bayan artabu da Sojoji

- Wadannan ‘Yan bindiga sun fara labewa a Kaduna da kuma Neja

- Sanatan Kaduna ya nemi ayi wani abu kafin su karasa cikin Abuja

Mun samu labari cewa fitaccen ‘Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya a yanzu, Shehu Sani, ya fito ya tabbatar da maganar da sojojin Najeriya su kayi kwanaki a game da ‘yan bindiga.

Sanata Shehu Sani yace maganar da Sojin kasar su kayi na cewa Miyagun da su ka addabi jama’a su na barin kuryar Arewa maso Yammacin kasar su na dumfarar jihohin Neja da kuma Kaduna mai makwabtaka da ita, a halin yanzu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 50 a Zamfara

Dole a takawa ‘Yan bindiga burki kafin su shigo Abuja – Shehu Sani

Shehu Sani ‘Yan bindigan da aka fatattaka daga Zamfara sun tsero Kaduna
Source: Twitter

‘Dan majalisar yace babu shakka wannan labari gaskiya ne domin kuwa Mutanen da ke zama a jejin Kamuku da kuma Alawa sun bayyana masu wannan. Shehu Sani ya nuna cewa babu karya a maganar da jami’an tsaron su kayi.

A shafin sa na Tuwita, Sanatan ya nemi jami’an tsaro su yi maza su yi maganin wadannan ‘yan bindiga da su ke hallaka mutane babu gaira-babu dalili, kafin su dura cikin wajen babban birnin tarayya Abuja da ke kan iyaka da jihar Neja.

Jami’an tsaro na Soji sun ce ‘Yan bindigan da aka fatattako daga cikin Zamfara su na samun mafaka ne a Kaduna, Kano da kuma jihar Neja, bayan dakarun musamman na Operation Harbin Kunama III sun lallasa wadannan Miyagu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel