Yadda kotu zata yanke hukunci tsakanin Buhari da Atiku

Yadda kotu zata yanke hukunci tsakanin Buhari da Atiku

-Kotu na kokarin raba gardama tsakanin Buhari da Atiku

-Akwai abubuwa da dama karkashin wannan kara kafin ya zama cewa an yanke hukunci a gaban kotu

Kotun sauraren korefe-korefen zabe dake Abuja da kuma kotun koli ta kasa za suyi bincike akan karar da jam’iyar adawa ta PDP ta shigar bisa kalubalantar nasarar APC a zaben shugaban kasan da ya gudana ranar 23 ga watan Fabrairu 2019.

Akwai sauran korefe-korefe guda uku daga wasu yan takarar jam’iyun adawa inda suke kalubalantar nasarar APC yayinda suke cewa an samu tangarda lokacin zaben wadanda suka sabawa dokokin zaben.

Yadda kotu zata yanke hukunci tsakanin Buhari da Atiku

Yadda kotu zata yanke hukunci tsakanin Buhari da Atiku
Source: UGC

KU KARANTA:Dangote yafi kowane dan Najeriya zuba jari a jami’o’in Najeriya, inji gwamnatin tarayya

Wadannan yan takarar uku sun hada da: Ambrose Owuru na jam’iyar HDP, Geff Chizee Ojinka na jam’iyar CC da kuma Aminchi Habu na jam’iyar PDM.

Manya ababen dubawa a nan sun kunshi:

Karfin ikon doka wanda kotu ke dashi

Sashe na 239 (1) na kudin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kotu damar yin kwakwaran bincike akan duk dan takarar da aka zaba matsayin shugaban kasa ko kuma mataimaki. Sashe na 134 (1) zuwa (3) na dokokin zabe ya bada mako uku bayan an fadi sakamakon zaben domin shigar da kara.

Hanyar bincike akan korafe-korafen da aka kawo

Kwamiti mai kunshe da mutum biyar wanda shugabar kotun daukaka kara ke jagoranta wato Zainab Bulkachuwa shine zai wannan binciken. A karkashin kulwarta zata saurari bayani daga bangarorin biyu da masu kara da kuma na masu kariya. Kotun korafe-korafen zabe nada hakkin bincike kayan da akayi aikin zaben dasu kana kuma ta saurari shaidu cikin lokacin da aka kebe domin yin hakan.

Manyan matsalolin kotun korafe-korafe da kuma ta koli

Shin wanda aka ayyana a matsayin yayi nasara a zaben shine yafi kowa samun yawan kuri’u?

Kotun korafe-korafe da ta koli zasu duba lamarin akan cewar jam’iyar APC da Buhari basu lashe zabe ba. Kamar yadda PDP ke kalubalanta duk da cewa APC ta samu kuri’a 15,191,847 inda PDP keda 11,262,978 daga jihohi 36 da kuma birnin tarayya.

Shin zaben ya cika sharuddan dokokin zabe?

Zai kasance akwai bincike da ya sahfi yadda zaben ya gudana. Shin mutum 2,906,384 basu samu damar yin zaben bane ko ya abin yake. Matsalar shigar da sakamako ne cikin EC8A, tantancewa kari ko ragi a cikin sakamakon, duk sun iya zamowa dalili.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel