Mutanen wani Kauye sun fito Gari sun tare Tawagar Mataimakin Shugaban kasa

Mutanen wani Kauye sun fito Gari sun tare Tawagar Mataimakin Shugaban kasa

Wassu fusatattun mutane sun tsare motar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a hanyar Umaru Musa Yar’adua a Abuja a safiyar yau Talata, 7 ga watan Mayu.

Mataimakin shugaban kasar ya kasance a hanyarsa ta zuwa tashan jirgin sama a lokacin da yan zanga zangan suka tsayar da tawagarsa a kauyen Goza.

Mazauna kauyen Gbagyi sun hadu a babban hanyar da ya hade tashan jirgin da birnin, don gudanar da zanga zanga akan shiga musu filayensu da sojoji suka yi.

Mutanen wani Kauye sun fito Gari sun tare Tawagar Mataimakin Shugaban kasa

Mutanen wani Kauye sun fito Gari sun tare Tawagar Mataimakin Shugaban kasa
Source: Twitter

Jami’an tsaron mataimakin shugaban kasa sun gaza kwantar ma masu zanga zangan hankula, har sai da mataimakin shugaban kasar ya sauko daga motarsa.

Wassu daga cikin masu zanga zangan sun yabi mataimakin shugaban kasar yayin da yake kokarin yi musu jawabi.

KU KARANTA KUMA: Peter Obi abokin takaran Atiku bai da lafiya, ya je asibiti

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Ministan kimiyya da fasaha a Najeriya, Dr Ogbonnaya Onu, ya fito ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ce za ta lashe zaben 2023 a yankin kasar Kudu maso Gabas idan lokacin zaben yayi.

Ogbonnaya Onu yace duba da yadda jam’iyyar ke da dinbin Magoya baya da kuma goyon-bayan da APC ke samu a kasar Ibo a halin yanzu, babu abin da zai hana jam’iyyar lashe zaben Najeriya mai zuwa nan da kusan shekara 4.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel