Satar mutane ita ce sabuwar sana'ar matasan Najeriya - Buhari

Satar mutane ita ce sabuwar sana'ar matasan Najeriya - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana garkuwa da mutane a matsayin sabon aikin yi ga matasan Najeriya

- A cewar shugaban kasar, ya bayyana cewa dawo da noman auduga da masaka zai taimaka matuka wurin samar da aikin yi a kasar nan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadin shi game da rashin tsaro a kasar nan. Shugaban kasar ya ce satar mutane ya zama sabon aikin yi ga matasan kasar nan.

A lokacin da ya ke magana jiya Litinin, 6 ga watan Mayu, 2019, a lokacin da ya ke raba irin auduga ga manoma dubu dari, wadanda za su yi noma a wannan shekarar a jihar Katsina, shugaba Buhari ya bayyana cewa matsalar tsaro a kasar nan na da alaka da rashin aikin yi ga matasa.

Shugaban kasar wanda ministan noma, Audu Ogbeh ya wakilta, ya bayyana cewa dawo da masana'antun da sana'ar saka a kasar nan zai taimaka sosai wurin samarwa matasa aikin yi.

Satar mutane ita ce sabuwar sana'ar matasan Najeriya - Buhari

Satar mutane ita ce sabuwar sana'ar matasan Najeriya - Buhari
Source: Twitter

Ya ce: "Kuskuren da muka aikata a baya ne ya ke dawo mana a wannan lokacin."

"Matasanmu su na gama karatu amma babu aikin yi. Wasu za su koma gida su koma barar katin waya, da kayan sawa, saboda babu masana'antu, ba a yin noma, babu aikin yi kwata-kwata kuma gwamnati ba za ta iya daukar ma'aikata ba saboda biyan na yanzu ma babu sauki a cikin shi," in ji shugaba Buhari.

KU KARANTA: Jerin abubuwa 20 da basa karya azumi

Ya kara da cewa matasan Najeriya sun koma sana'ar satar mutane, satar shanu da sauran nau'i na ayyukan ta'addanci, kuma hakan ya na sanya tsoro a zuciyar dukkanin 'yan Najeriya.

Idan ba a mance ba majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton yadda fadar shugaban kasa ta nuna damuwarta akan sace Hakimin Daura, Alhaji Musa Umar, wanda ya ke siriki ga babban dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel