‘Yan Majalisan Akwa Ibom da su ka tsere daga PDP sun samu nasara a Kotu

‘Yan Majalisan Akwa Ibom da su ka tsere daga PDP sun samu nasara a Kotu

A jiya, Litinin 6 ga Watan Mayu ne wani babban Kotun tarayya da ke zama a Garin Uyo a cikin jihar Akwa Ibom, ta bada umarnin a dawo da wasu ‘yan majalisar dokoki zuwa kan kujerun su.

Kwanakin baya, Kakakin majalisar dokokin jihar Akwa Ibom, Rt. Hon. Onofiok Luke ya yanke hukuncin cewa wasu ‘yan majalisa za su bar kujerunsu. Yanzu kotu ta fito tace dakatarwar da aka yi masu ya sabawa dokar kasa.

Honarabul Onofiok Luke ya karbe kujerun wasu ‘Yan majalisan jihar ne da su ka sauya-sheka daga PDP zuwa APC a cikin Watan Nuwamba. Babban kotu tace babu wanda ya isa ya raba ‘yan majalisan daga kan kujerunsu sai Alkali.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta nemi Jami’an tsaro su saki babban Sanatan ta

‘Yan Majalisan Akwa Ibom da su ka tsere daga PDP sun samu nasara a Kotu

Alkali ya fadawa Majalisar Akwa Ibom ta dawo da wadanda su ka sauya-sheka
Source: Twitter

Daga cikin ‘yan majalisar da aka dakatar bayan sun koma APC akwai: Hon Nse Ntuen, Hon Victor Udofia, Hon Idongesit Ituen, Hon Gabriel Toby da kuma Hon Otobong Ndem. Kotu tace a maida dukkan su kan kujerun da su ke kai.

Alkali mai shari’a F. O. Riman ya bayyana cewa shugaban majalisar bai isa ya dakatar da wadannan ‘yan majalisa don kurum sun canza jam’iyya ba. Alkalin ya nemi a biya ‘yan majalisar duk albashin su da alawus da su ka rasa.

A karar da aka kai gaban kotun mai lamba FHC/UY/CS/171, Alkali F. O. Riman ya bada umarni a kyale wadannan ‘yan majalisa su koma ofisoshinsu su cigaba da aiki, sannan kuma za su cigaba da halartar zama a zauren majalisa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel