Peter Obi abokin takaran Atiku bai da lafiya, ya je asibiti

Peter Obi abokin takaran Atiku bai da lafiya, ya je asibiti

- Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi bai da lafiya

- Obienyemm, hadimin Obi, yace ubangidan nasa ya ziyarci asibiti a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu

- Abokin takaran Atiku ya bayyana cewa yana iya ziyartan kowani asibiti a kasar a duk lokacin da yake rashin lafiya

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu ya ziyarci asibitin Queen of the Rosary, da ke waterside, Onitsha, inda aka yi masa gwaje-gwaje da ganin likita.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Valentine Obienyem hadiminsa ya bayyana cewa ya koma gidansa kuma kamar koda yaushe kai tsaye ya zarce ga aiki.

Peter Obi abokin takaran Atiku bai da lafiya, ya je asibiti

Peter Obi abokin takaran Atiku bai da lafiya, ya je asibiti
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Obienyem yace Obi ya ziyarci asibitin a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, inda ya kara da cewa yayi korafin cewa yana jin zazzabi.

A cewarsa, "A yau da na shiga gidan da misalin karfe 7:30 am babu abunda ya chanja), an sanar dani cewa ya tafi asibitin Queen of the Rossary, Wataerside, Onitsha. Ba da jimawa ba ya dawo.

KU KARANTA KUMA: Ramadan: Ba za mu amince da wa’azin batanci ba – APC ta gargadi malamai

"Asibitin Anambra da aka yasar bayan gwamnati ta saki N25m don gyara na ji cewa ya tafi asibitin, ya ga likita sannan aka dibi jininsa don gwaje-gwaje. Kamar kullun, kai tsaye ya koma bakin aiki koda dai iana sauraron cewa babu mamaki likita ya shawarce shi da ya huta. Muna bakin aiki har sai da muka tashi zuwa Lagas a wannan ranar. Kamar kowani mutum, yana rashin lafiya."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel