Messi zai kai har shekaru 45 kafin ya daina buga tamola - Bartomeu

Messi zai kai har shekaru 45 kafin ya daina buga tamola - Bartomeu

Babban jagoran kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Josep Bartomeu, ya ce akwai yiwuwar fitaccen dan wasan kungiyar, Lionel Messi zai kai har shekaru 45 na rayuwar sa gabanin ya daina shura tamola.

Lionel Messi

Lionel Messi
Source: UGC

Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa, a yayin da Messi ya tsawaita kwantiragin sa da kungiyar Barcelona daga shekarar 2017 zuwa 2021, Bartomeu ya ce dan wasan zai iya shafe wani zamanin gabanin ya yi ritaya daga taka leda.

A kakar kwallon kafa ta bana, Messi ya taimakawa kungiyar sa ta Barcelona wajen zura kwallaye 48 cikin dukkanin gasar kwallon kafa da ta ke bugawa a yanzu.

A ranar Larabar da ta gabata ne dan wasa Messi ya jefa kwallo ta 600 ga kungiyar sa ta Barcelona yayin wasan kofin zakarun turai da ta kara da kungiyar Liverpool wadda ta sha kashin gaske da ci uku da nema.

KARANTA KUMA: Annobar Yunwa na yiwa 'Yan Boko Haram dauki dai-dai - BMO

Yayin wasan na gasar kofin zakarun Turai da aka kara a filin wasanni na Barcelona watau Camp Nou da ke kasar Andalus, Messi ya jefa kyawawan kwallaye biyu a mintuna na 72 da kuma 82 cikin komar kungiyar Liverpool.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na da fifiko na rinjayen samun nasara yayin karashen wasa a zagaye na biyu da za ta kara da kungiyar Liverpool a filin wasannin ta na Anfield da ke kasar Ingila a wannan mako.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel