Wasu sun fara lissafin yadda za su samu mulki a APC a 203 tun yanzu – inji El-Rufai

Wasu sun fara lissafin yadda za su samu mulki a APC a 203 tun yanzu – inji El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yace rikicin cikin-gidan da aka rika samu a jam’iyyar APC mai mulki a daf da zaben 2019, bai rasa nasaba da dogon burin wasu daga cikin ‘Ya ‘yan jam’iyyar.

Malam Nasir El-Rufai yake cewa harin mulki a shekarar 2023 da wasu su ke yi ne ya jawo rikicin da jam’iyyar APC ta shiga a lokacin zaben bana. Gwamnan yace wasu su na kokarin yadda za su tunkari zaben 2023 a cikin APC.

Gwamnan na jihar Kaduna ya nuna takaicin sa game da wasu daga cikin kusoshin da APC ta rasa a 2019, inda kuma yace bai kamata wasu su rika hangen 2023, yayin da shugaba Buhari bai soma wa’adin sa na biyu ba ma tukun.

El-Rufai yake cewa dole shugaba Buhari ya dauki mataki mai tsauri ya hukunta masu irin wannan dogon buri a cikin jam’iyyar domin kuwa za su iya kawo masa matsala a wannan karo saboda abin da su ke hari a zaben na 2023.

KU KARANTA: Jamiyyar APC ce za ta lashen lashe zaben 2019 inji Ministan Buhari

Wasu sun fara lissafin yadda za su samu mulki a APC a 203 tun yanzu – El-Rufai

Gwamnan Kaduna yace akwai wadanda 2023 ya rufewa idanu a APC
Source: Depositphotos

Gwamna El-Rufai yayi duk wannan jawabi ne a Birnin Ikoyi da ke cikin jihar Legas lokacin da yake zantawa da Attajirai da ‘Yan kasuwa. El-Rufai yace rigimar da ta barke a APC ba ta da alaka da zaben bana, sai dai harin zaben 2023.

Malam El-Rufai yace ‘yan siyasa su na da dogon lissafi da hangen nesa don haka wasu a APC su ka fara hankoron zaben 2023, wanda hakan ya jawowa APC ta rasa wasu jihohi a zaben da aka yi, Gwamnan yace dole Buhari ya dauki mataki.

A jawabin gwamnan, yake cewa ya kamata ‘yan siyasar kasar su zauna tare da juna su ajiye banbamcin su domin ganin abin da ya dace da cigaban Najeriya. El-Rufai yace wannan ne kurum zai sa kasar ta cigaba kamar sauran kasashe.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel